Yanzu-yanzu: IGP Ibrahim Idris ya shiga ganawar sirri da shugaba Buhari

Yanzu-yanzu: IGP Ibrahim Idris ya shiga ganawar sirri da shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga ganawar gaggawa da sifeto janar na hukumar yan sanda, IGP IBrahim Kpotum Idris.

An fara wannan ganawar misalin karfe 2:30 bayan Sallar Juma'a cikin ofishin shugaban kasa dake fadar shugaban kasa ta Aso Villa, birnin tarayya Abuja.

Ya kamata Sifeto Janar din ya yi murabus daga aikin yan sanda bayan cika shekaru sittin da haihuwa amma ana kyautata zaton cewa shugaba Buhari zai kara masa wa'adi.

Wata majya mai karfi ta bayyanawa manema labarai cewa abinda Buhari zai yi zai bayyana bayan ganawar da sukeyi a yanzu.

Mun kawo muku rahoton cewa rashin tabbas ya mamaye hukumar yan sandan Najeriya kan abinda zai faru a gidan hukumar yayinda wa'adin babban sifeto janar na yan sanda, Ibrahim Kpotum Idris, ya kare jiya.

KU KARANTA: Jam'iyyar PDP ta samu gagarumin karuwa a jihar Gombe

IGP Ibrahim Idris ne shugaban hukumar yan sanda na 19 a tarihin hukumar, wanda shugaba Muhammadu Buhari ya nada ranan 21 ga watan Maris, 2016 domin maye tsohon IG, Solomon Arase.

Ya shiga hukumar yan sandan Najeriya ne a shekarar 1984 kuma ya cika shekaru 34 da aiki a wannan hukuma.

Amma korafe-korafe da maganganu sun fara kwarara daga kungiyar fafutuka da jam'iyyar PDP kan cewa kada shugaba Buhari ya sake ya karawa IGP Ibrahim Idris wa'adi, kawai ya nada wani sabon IGP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel