Jam'iyyar PDP ta samu gagarumin karuwa a jihar Gombe

Jam'iyyar PDP ta samu gagarumin karuwa a jihar Gombe

Jam'iyyar Peoples Democratic Party a jihar Gombe ta samu gagarumin karuwa yayinda akalla mambobin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, 3000 suka fita daga jam'iyyar a karamar hukumar Deba dake jihar.

Mambobin jam'iyyar APC daga garuruwan Lubo, Kinafa da Difa sunyi hannun riga da jam'iyyar ne yayinda ake shirye-shiryen zaben shugaban kasa, yan majalisun tarayya da na gwamna a jihar a watan Febrairu, 2019.

Kakakin majalisar dokokin jihar da wasu manyan jami'an gwamnatin jihar sun tarbi wadanda suka sauya sheka. Sun bayyana cewa suna canza jam'iyya ne saboda irin ayyukan zo a gani da gwamnan johar Ibrahim Dankwambo keyi.

KU KARANTA: Atiku makiyin kabilar Fulani ne, kada wanda ya zabeshi - Miyetti Allah Kautal Horey ta yi kira ga mambobinta

A bangare guda, Mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da suka sauya sheka zuwa All Progressives Congress (APC) a kauyen Tika da ke yankin Kuje, sun shugabansu, Abdullahi D. Galadima, cewa sun yi danasanin kuskuren da suka yi a zabar jam’iyyar adawa a zaben da ya gabata.

Wani tsohon shugaban PDP a Tika, Mista Ayi Gyiayegbe, ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci mambobin PDP 1,245 zuwa APC a jiya, a yankin cewa ba za su maimaita irin wannan kuskuren ba a zaben Fabrairu da Maris.

Yace hukuncin da ya yanke na komawa APC daaga PDP saboda tarin kokarin da gwamnatin Galadima tayi ne a Kuje, inda ya bayyana cewa shugaban ya taimaki mutane da dama a yankin duk da banbancin siyasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel