Yanzu-yanzu: Tsohon gwamnan jihar Kano, Hamza Abdullah, ya rasu

Yanzu-yanzu: Tsohon gwamnan jihar Kano, Hamza Abdullah, ya rasu

Labarin da muka samu yanzunnan na nuna cewa Allah ya yiwa tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan birnin tarayya, AVM Hamza Abdullahi rasuwa.

Tsohon sojan ya rasu ne a kasar Jamus ranan Laraba, 2 ga watan Junairu, 2018.

AVM Hamza Abdullahi ya kasance gwamnan mulkin soja ne tsakanin shekarar 1984 da 1985 yayinda shugaba Muhammadu Buhari ke mulkin kasar.

Yanzu-yanzu: Tsohon gwamnan jihar Kano, Hamza Abdullah, ya rasu

Yanzu-yanzu: Tsohon gwamnan jihar Kano, Hamza Abdullah, ya rasu
Source: Facebook

Marigayi Hamza Abdullahi haifaffen garin Hadejia ne a jihar Jigawa. An haifeshi ranan 2 ga watan Maris, 1945. Ya rasu a wani asibitin kasar Jamus bayan wata gajeruwar rashin lafiya da yayi.

Ya rasu ya bar mata uku da yara.

Kakakin masarautar Hajejia, Mohammed Garba Talak ya tabbatar da labarin. Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Abubakar ya mika sakon ta'aziyyarsa inda ya ce Najeriya ta yi babban rashi.

A jawabin da hadimin gwamnan, Mallam Bello Zaki, ya saki, gwamnan yave: "Marigayin ya kasance mutumin arziki kuma dattijon arziki wanda ya taka rawar gani wajan kafa tsohuwar jihar Kano."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel