Yanzu-Yanzu: Wani jirgin yakin sojojin saman Najeriya ya yi hatsari a Baga

Yanzu-Yanzu: Wani jirgin yakin sojojin saman Najeriya ya yi hatsari a Baga

Rundunar sojojin saman Najeriya da yanzu haka ke yaki da 'yan ta'addan kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram ta ce wani jirginta mai saukar ungulu ya yi hatsari yayin yaki da masu tayar da kayar baya a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Sanarwar da mai magana da yawun sojin kasar Ibikunle Daramola ya fitar, ta ce daman jirgin mai saukar ungulu ya na taimakawa dakarun sojin kasa ne da ke yaki da 'yan Boko Haram lokacin da abin ya faru a garin Damasak da ke jihar Borno da maraicen jiya Laraba.

Yanzu-Yanzu: Wani jirgin yakin sojojin saman Najeriya ya yi hatsari a Baga

Yanzu-Yanzu: Wani jirgin yakin sojojin saman Najeriya ya yi hatsari a Baga
Source: Twitter

KU KARANTA: Yan bindiga sun sake kai mummunan hari a Zamfara

Legit.ng Hausa ta samu cewa sanarwar bata bayyana musabbabin faduwar jirgin ba, da kuma mutanen da ke cikinsa lokcin da ya yi hatsrin da ko an yi hasrar rayuka ko jikkata.

A baya-bayan nan sojojin Najeriya sun zafafa kai hare-hare maboyar 'yan Boko Haram, a yankin na arewa maso gabashin kasar.

Hakan na faruwa ne a didai lokacin da su ma 'yan Boko Haram, da mayakan da sukai mubaya'a ga myakan IS suke ci gaba da kai munanan hare-hare a yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel