Kowa yabi: Nuhu Ribadu ya bada motoci, ofis domin yakin neman zaben Buhari (Hotuna)

Kowa yabi: Nuhu Ribadu ya bada motoci, ofis domin yakin neman zaben Buhari (Hotuna)

Tsohon shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC kuma babban jigon jam'iyyar APC a jihar Adamawa, Nuhu Ribadu, ya bada kyautan motoci da ofis matsayin gudunmuwarsa wajen yakin neman zaben shugaba Muhammmadu Buhari a 2019.

Malam Ribadu ya mika wannan ofishi da ya kafa da motoci da yayi niyyar yakin neman zaben gwamnan jihar Adamawa ga Buhari a ranan Litinin, 31 ga watan Disamba, 2019.

Game da cewarsa, zaben da za'ayi a watan Febrairu zabi ne tsakanin abubuwan da gwamnatin baya sukayi da ba za'a taba mantawa da su ba, da kuma wannan sabuwar gwamnatin gaskiya da amana.

Kowa yabi: Nuhu Ribadu ya bada motoci, ofis domin yakin neman zaben Buhari (Hotuna)

Kowa yabi: Nuhu Ribadu ya bada motoci, ofis domin yakin neman zaben Buhari (Hotuna)
Source: Facebook

Yace shi da mabiyansa za suyi aiki tukuru domin tabbatar da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya lashe zabe a jihar Adamawa.

Ya yi kira ga masoya jam'iyyar APC a jihar su ninka kuri'un da shugaba Buhari ya samu a zaben 2015.

Yace:"Akwai zabi tsakanin yan Najeriyan gaskiya. Babu wanda zai so ya mayar wadannan fuskokin mutanen da suka dukufar da kasar nan. Mun cigaba, ba zamu yarda su mayar damu baya ba."

"A shekaru uku da suka gabata, EFCC da sauran hukumomi sun dukufa suna kwato kudaden sata cikin lokaci kalilan."

"Muna farin cikin cewa wannan satan ya daina faruwa. Kada mu bari wadanda sata ba komai bane a wajensu su dawo su cigaba da abinda suka saba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel