Zamu iya kawar da ta'addanci a 2019 - Atiku

Zamu iya kawar da ta'addanci a 2019 - Atiku

- An tattaro cewa manyan jam’iyyar na fushi da Atiku cewa tun bayan da ya lashe zaben fidda gwani sai ya yasar da kowa

- Atiku yace zai fitar mutane miliyan 50 daga talauci daga shekarar 2019

Dan takaran shugaban kasan Najeriya karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya yi kira ga yan Najeriya da bayar da goyon baya wajen kawo karshin ta'addanci a shekarar 2019.

Atiku ya bayyana hakan ne sakon murnan shirin shiga sabuwar shekarar 2019.

KU KARANTA: Hotunan ta'aziyyar da Shugaba Buhari ya kai jihar Sokoto

Yace: "Da shugabanci na kwarai, shekarar 2019 zata iya zama shekarar da zamu kawo karshen ta'addanci da samar da zaman lafiya."

"Yayinda shekarar 2018 ta zo karshe muka muka nufi 2019, a madadin kaina da iyalaina, ina tayaku murnan shiga sabuwar shekara."

"A shekarar 2018, mun zama hedkwatan talauci a duniya, amma ina kyautata zaton cewa a shekarar 2019, idan muka zabi sabuwar gwamnati, zamu iya zama hedkwatan kokarun cire mutanenmu daga cikin talauci."

Mun kawo muku rahoton cewa Wani gwamnan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya yi gargadin cewa jam’iyyarsa na iya faduwa zaben shugaban kasa a 2019 idan har bata magance wasu lamura da ke dawo day akin neman zaben ta baya ba.

Gwamnan wanda ya bukaci a boye sunansa ya fada ma jaridar Premium times cewa shirye-shiryen zaben shugaban kasa da PDP ke yi na cike da kalubale.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel