Gwamnan PDP yace Atiku na iya faduwa a zaben 2019

Gwamnan PDP yace Atiku na iya faduwa a zaben 2019

- Wani gwamnan PDP ya yi gargadin cewa jam’iyyarsa na iya faduwa zaben shugaban kasa a 2019 idan har bata magance wasu lamura da ke yawo cikinta ba

- An tattaro cewa manyan jam’iyyar na fushi da Atiku cewa tun bayan da ya lashe zaben fidda gwani sai ya yasar da kowa

- Daga cikin jiga-jiagan jam’iyyar dake fushi da salon jagorancin sa sun hada da gwamnonin, Gombe, Ribas, Sokoto, Sule Lamido, Ahmed Makarfi, da Rabiu Kwankwaso

Wani gwamnan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya yi gargadin cewa jam’iyyarsa na iya faduwa zaben shugaban kasa a 2019 idan har bata magance wasu lamura da ke dawo day akin neman zaben ta baya ba.

Gwamnan wanda ya bukaci a boye sunansa ya fada ma jaridar Premium times cewa shirye-shiryen zaben shugaban kasa da PDP ke yi na cike da kalubale.

Gwamnan PDP yace Atiku na iya faduwa a zaben 2019
Gwamnan PDP yace Atiku na iya faduwa a zaben 2019
Asali: Depositphotos

An tattaro cewa manyan jam’iyyar na fushi da Atiku cewa tun bayan da ya lashe zaben fidda gwani sai ya yasar da kowa, yin abin da yaga dama yake yi ba tare da neman shawarar wani dan jam’iyya ba, ko kai waye.

Wasu daga cikin jiga-jiagan jam’iyyar dake fushi da salon jagorancin sa sun hada da gwamnonin, Gombe, Ribas, Sokoto, Sule Lamido, Ahmed Makarfi, da Rabiu Kwankwaso.

KU KARANTA KUMA: Za a hukunta duk wanda aka kama yana amsar cin hanci - Buhari

Wani babban katobara da yayi shine yin gaban kansa wajen zaban mataimakin sa batare da ya tuntubi ‘yan jam’iyyar ba.

Bayannan gwamnan yace, nada irin su Fayose matsayi maigirma a kamfen din matsala ce domin babu wanda zai saurari Fayose a yankin ‘yarbawa sannan Saraki ma jakar sa cike take fam da matsaloli.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel