Boko Haram sun kwace garuruwa 6 a Borno

Boko Haram sun kwace garuruwa 6 a Borno

- Rahotanni sun nuhna cewa yan ta’addan Boko Haram sun kwace garuruwa shida a jihar Borno

- Garuruwan sune Baga, Doron-Baga, Kross Kawwa, Bunduran, Kekeno da kuma Kukawa

- Wuraren sun kasance manyan cibiyoyi a karamar hukumar Kukawa da ke yankin arewacin Borno

Rahotanni da ke zuwa mana sun yi ikirarin cewa yan ta’addan Boko Haram sun kwace garuruwan Baga, Doron-Baga, Kross Kawwa, Bunduran, Kekeno da kuma Kukawa a jihar Borno.

Daily Trust ta ruwaito cewa wata babbar majiya ta sojoji da siyasa ne suka bayyana hakan a Maiduguri a ranar Lahadi, 30 ga watan Disamba.

Boko Haram sun kwace garuruwa 6 a Borno
Boko Haram sun kwace garuruwa 6 a Borno
Asali: Depositphotos

An tattaro cewa dukkanin garuruwan guda shida sun kasance manyan cibiyoyi a karamar hukumar Kukawa da ke yankin arewacin Borno a yanzu haka babu dan Najeriya ko wata runduna a yankunan.

Yan ta’addan sun fara kai hari wani sansani na rundunar tsaro da ke Mil Hudu (wani yanki a wajen garin Baga) da misalin karfe 4pm sannan sojoji suka mayar da martani.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin sama ta yi watsa-watsa da mabuyar yan ta’adda kusa da Baga

Rahoton ya kuma yi ikirariun cewa ana ta arangama har tsakar dare inda daga bisanin yan ta’addan suka kwace sansanin ojin yayinda sojojinmu suka ja da baya.

An kawo cewa kwamandan rundunar, wanda aka bayar da sunansa a matsayin Birgediya Janar Hassan ya tsere cikin dare zuwa wani sansani na yan sanda da ke garin Baga tare da wasu jami’ansa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel