Yanzu Yanzu: Rundunar soji ta kau da yan kunar bakin wake mata su 3

Yanzu Yanzu: Rundunar soji ta kau da yan kunar bakin wake mata su 3

- Dakarun soji a sun kawar da yan kunar bakin wake mata su uku, yayinda suke sintiri a kewayen kauyen Kubtara da ke karamar hukumar Dikwa na jihar Borno

- Rundunar ta kuma samo wani karamin bam da rigar kunar bakin wake a wajen da lamarin ya afku

- Shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Tukur Buratai ya yaba ma dakarun sojin akan nasarar da suka yi wajen hana faruwar lamarin

Rundunar soji a ranar Lahadi, 30 ga watan Disamba sun kawar da yan kunar bakin wake mata su uku, yayinda suke sintiri a kewayen kauyen Kubtara da ke karamar hukumar Dikwa na jihar Borno.

Wata sanarwa daga Kanal Onyema Nwachukwu, mataimakain daraktan labarai na Operation Lafiya Dole a ranar Litinin ya bayyana cewa rundunar ta kuma samo wani karamin bam da rigar kunar bakin wake a wajen da lamarin ya afku.

Yanzu Yanzu: Rundunar soji ta kau da yan kunar bakin wake mata su 3

Yanzu Yanzu: Rundunar soji ta kau da yan kunar bakin wake mata su 3
Source: UGC

Nwachukwu ya bayyana cewa shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Tukur Buratai ya yaba ma dakarun sojin akan nasarar da suka yi wajen hana faruwar lamarin.

Buratai ya karfafa masu gwiwa kan cewa su kasance masu lura sosai da jajircewa yayinda suke kakkabe sauran ta’addan na Boko Haram.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa ba a binne Shagari a Hubbare ba

A baya mun ji cewa rundunar sojojin saman Najeriya a jiya Lahadi, 30 ga watan Disamba tace tawagarta na Operation Lafiya Dole sun hallaka yan ta’addan Boko Haram da dama a mabuyarsu da ke kusa da yankin Baga a arewacin jihar Borno.

A wani jawabi daga kakakin rundunar sojin saman Air Commodore Ibikunle Daramola ya bayyana cewa na kaddamar da harin ne a ranar Asabar bayan tawagar kwararru na rundunar sun gano yan ta’addan a inda suka taru a karkashin wasu bishiyoyi a kewayen kogon kiwon kifi kusa da Baga.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel