Rundunar sojin sama ta yi watsa-watsa da mabuyar yan ta’adda kusa da Baga

Rundunar sojin sama ta yi watsa-watsa da mabuyar yan ta’adda kusa da Baga

- Rundunar sojojin saman tace tawagarta na Operation Lafiya Dole sun hallaka yan ta’addan Boko Haram da dama a mabuyarsu da ke kusa da yankin Baga a arewacin jihar Borno

- An kaddamar da harin bayan tawagar kwararru na rundunar sun gano yan ta’addan a inda suka taru a karkashin wasu bishiyoyi a kewayen kogon kiwon kifi kusa da Baga

- Kakakin rundunar sojin saman Air Commodore Ibikunle Daramola ne ya bayyana hakan a wani jawabi da ya saki

Rundunar sojojin saman Najeriya a jiya Lahadi, 30 ga watan Disamba tace tawagarta na Operation Lafiya Dole sun hallaka yan ta’addan Boko Haram da dama a mabuyarsu da ke kusa da yankin Baga a arewacin jihar Borno.

Rundunar sojin sama ta yi watsa-watsa da mabuyar yan ta’adda kusa da Baga
Rundunar sojin sama ta yi watsa-watsa da mabuyar yan ta’adda kusa da Baga
Asali: Depositphotos

A wani jawabi daga kakakin rundunar sojin saman Air Commodore Ibikunle Daramola ya bayyana cewa na kaddamar da harin ne a ranar Asabar bayan tawagar kwararru na rundunar sun gano yan ta’addan a inda suka taru a karkashin wasu bishiyoyi a kewayen kogon kiwon kifi kusa da Baga.

Yace: “Rundunar sojin, sun yi amfani da jirgin sama na yaki wajen kai hari wajen. Harin da suka kaddamar akai-akai ya kashe yan ta’adda da dama sannan wasu sun ji mumunan rauni. An kakkabe sauran yan ta’addan da suka tsira a wani hari da aka sake kaddamarwa daga bisani."

A baya mun ji cewa Hukumar Sojin Najeriya ta sanar da cewa tana shirin kwashe mutanen Baga da ke jihar Borno zuwa wasu garuruwan dubba da irin atisayen da dakarun sojin su keyi a garin a cikin 'yan kwanakin nan.

Hukumar Sojin ta ce za ta gudanar da wannan aikin ne tare da hadin gwiwa da gwamnatin jihar Borno.

KU KARANTA KUMA: Zan hukunta duk wanda aka samu da hannu a rikicin Kasuwar Magani – El-Rufai

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel