'Yar baiwa: Labarin wata kykkyawar budurwa 'yar shekaru 24 dake tuka jirgi daga Arewa

'Yar baiwa: Labarin wata kykkyawar budurwa 'yar shekaru 24 dake tuka jirgi daga Arewa

Tukin jirgi dai na daya daga cikin sana'o'in da ake ta'allaka ta da jin sin maza kadai ko a yammacin duniya ballantana kuma ma a nahiyar Afrika, musamman ma a arewacin Najeriya da ake kallon akwai masu ra'ayin rikau sosai.

Sai dai wannan tunanin ka iya zama gurgu musamman ma idan aka yi duba na tsakani ga labarin da muke dauke da shi yau na wata matashiyar kykkyawar budurwa mai shekaru 24 kacal a duniya daga jihar Borno da ta karanci tukin jirgi kuma tana yi.

'Yar baiwa: Labarin wata kykkyawar budurwa 'yar shekaru 24 dake tuka jirgi daga Arewa

'Yar baiwa: Labarin wata kykkyawar budurwa 'yar shekaru 24 dake tuka jirgi daga Arewa
Source: Facebook

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun murkushe harin 'yan ta'adda a Baga

Legit.ng Hausa ta samu cewa daga cikin firar da tayi da majiyar mu, Maira Umar Bishir tace tana sha’awar karance-karance da tafiye-tafiye tun tana 'yar karama wanda hakan bai rasa nasaba da irin rayuwar da ta tsinci kanta a ciki yanzu.

Haka zalika Maira Umar Bishir tace ita ko kadan bata sha wahala ba wajen shawo kan mahaifan ta kafin su amince su bar ta tayi karatun inda tace sun mai karfafa mata gwuiwa sosai wajen ganin mafarki na ya tabbata.

Da aka tambaye ta ko ya mutane suka ji lokacin da suka ganta akaran farko matsayin mai tuka jirgin sama sai ta ce sun yi mamaki matuka kasancewar ta mace kuma daga arewacin Nijeriya, musamman yadda mahaifan ta suka yarda da ta yi wannan karatu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel