'Yan bangar siyasa kadai na ke sayarwa da tabar wiwi a jihar Neja - Matashi

'Yan bangar siyasa kadai na ke sayarwa da tabar wiwi a jihar Neja - Matashi

Hukumar 'yan sanda ta Najeriya reshen jihar Neja, ta cafke wani Matashi mai kimanin shekaru 28 a duniya, Isah Aliyu, cikin unguwar Daji dake birnin Minna. Isah ya shiga hannun jami'an tsaro dauke buhunan tabar wiwi kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

'Yan bangar siyasa kadai na ke sayarwa da tabar wiwi a jihar Neja

'Yan bangar siyasa kadai na ke sayarwa da tabar wiwi a jihar Neja
Source: Twitter

Matashin ya shaidawa manema labarai na Northern City News cewa, ya kasance daya daga cikin mutune biyar da suka shahara tare da kaurin suna wajen sayar da kayen maye ga Matasa a garin Maitumbi da kewayensa.

Cikin kalaman sa yake cewa, "sun saba sayar da tabar wiwi musamman Matasa karnukan Siyasa domin duk inda suka dira su tayar da tarzoma."

"A halin yanzu da zaben 2019 ya gabato, ido zai bude a kasuwar mu da ko shakka ba bu zamu samu riba mai girman gaske yayin da Matasa za su ribaci hajar da muke sayarwa.

KARANTA KUMA: Gwamnati ta aurar da Marayu 270 a jihar Jigawa

Aliyu yayin ganawarsa da manema labarai ya bayyana cewa, akwai riba mai girman gaske cikin sana'ar sa ta sayar da tabar wiwi ga Matasa da ya sanya ya yi watsi da duk wani aikin wahala ta ribar sa ba ta taka kara ballantana ta karya shi ba.

Jami'in hulda da al'umma na hukumar 'yan sandan, Muhammad Abubakar, ya zayyana yadda Aliyu ya amsa laifin sa na kasancewa daya daga cikin miyagun da suka addabi al'ummar unguwar Daji wajen sayar da kayan maye nau'ika daban-daban.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel