Tsawon shekaru 40, sau 2 kadai na taba rikici da matata Maryam - IBB

Tsawon shekaru 40, sau 2 kadai na taba rikici da matata Maryam - IBB

Ga mutum kamar Ibrahim Babangida, wanda ya shugabanci Nigeria kuma ya taka tsaunin nasara mai yawa, kuma kasancewarsa Musulumi, wanda addini ya yarje masa ya auri har mata hudu. Amma yaki yiwa matarsa tilo, Mrs Maryam Babangida kishiya har ta bar duniya a ranar 27 ga watan Disambar 2009.

A zantawarsa da jaridar Tribune, Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana yadda zamansa da Maryam ya kasance na tsawon shekaru 40 da suka kwashe a matsayin mata da miji, tun daga rayuwarsa ta soja har kawo lokacin mutuwarta.

IBB ya bayyana cewa, ya kasance matashi a lokacin dan kwalisa, wanda zai yi wuya mace ta ganshi bata kyasa ba. Don haka, ya karanci yadda rayuwa take tafiya tun kafin yayi aure, ya karanci sauki da wahalar da ke cikin zamantakewar aure.

KARANTA WANNAN: Adikon Zamani: Matakai 7 na dorewar tsoho da sabon aure

Tsawon shekaru 40, sau 2 kadai na taba rikici da matata Maryam - IBB
Tsawon shekaru 40, sau 2 kadai na taba rikici da matata Maryam - IBB
Asali: Depositphotos

A cewarsa, basu wani jima sosai shida Maryam suna soyayya ba, kasancewar ta mallaki duk wasu ka'idoji da yake son matar da zai aura ta mallaka, don haka bai bata wani lokaci ba wajen neman aurenta, har aka daura masu aure.

Ko da aka tambaye shi ka'idojin da Maryam ta cika kafin ya aureta, Babangida ya ce: "Ta kasance macen da take sona a yadda nake, ba wai don wani abu da na mallaka ba, a'a, ni take so.

"Na kasance dai mutum kamar kowa, ina da nawa kura kuran. Ina aikata kuskure kuma idan har ka shirya zama dani a haka, to bani da matsala. Ita kuwa Maryam ta karance ni a haka, wannan ne yasa zamantakewarmu ta yi karko.

"A tsawon shekaru 40 da muka shafe a matsayin miji da mata, zan iya tabbatar maka cewa sau 2 ne kacal muka taba samun sabani. Ita ta kasance mace mai tsantsani da saukin kai, kuma iyayenta masu fahimta ne. Kullum suna goyon bayana," a cewar Ibrahim Babangida.

Dangane da rayuwarsa ta soja, da yadda Maryam tayi hakurin zama da shi, IBB ya buga misali da lokutan da kasar ke cikin yaki, inda yake shafe tsawon lokaci bai dawo gida ba, kullum suna fagen yaki, kuma akwai tsammani da zullumi da yawa.

"Tana kasancewa cikin zullumi, ko zan dawo da raina? Ko dai za a kashe ni a can? Ire iren wadannan tunanikan na ziyartar zuciyarta. Sai dai ta kasance mace mai dakakkar zuciya kuma mai sanya kyakkyawan tsammani, na cewar tabbas zan koma gareta da raina. Kuma da haka ta raini yaranmu har suka girma."

IBB ta tabbatar da cewa tsawon shekaru 40 na aurensu, matarsa Maryam bata taba zuwa gidansu da suna taje 'yaji' ba, wai ko don bacin rai ko wani abu makamancin hakan. Wannan ne ma ya kara jaddada cewa sau biyu kacal ne ya taba samun sabani da ita, kuma cikin sauki suka warware komai tsakaninsu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel