Aiki sai mai shi: An soma aikin gina sabuwar tashar jiragen ruwa a Najeriya

Aiki sai mai shi: An soma aikin gina sabuwar tashar jiragen ruwa a Najeriya

An kaddamar da aikin gina tashar jiragen ruwa cikin ruwa mai zurfi ta Lekki a jihar Legas ta kasar Najeriya a jiya Alhamis. Bayan kammala aikin, tashar za ta zama irinta mafi girma a yankin kudu da hamadar Sahara.

Tashar kuma za ta kawo karshen tarihin kasar Najeriya na rashin samun tashar jirgin ruwa da ke samun ruwa mai zurfi.

Aiki sai mai shi: An soma aikin gina sabuwar tashar jiragen ruwa a Najeriya

Aiki sai mai shi: An soma aikin gina sabuwar tashar jiragen ruwa a Najeriya
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Jerin girma da yadda mukamai suke a gidan soja

Legit.ng Hausa ta samu cewa mataimakin shugaban kasar Najeriya Yemi Osinbajo da ya halarci bikin kaddamar da aikin, ya ce wannan sabuwar tashar jiragen ruwa za ta haifar da karin moriya ga yankin ciniki cikin 'yanci na Lekki.

Yayin da a nasa bangare, Rotimi Amaechi, ministan sufuri na kasar, ya ce wannan tasha za ta taimaka wajen tabbatar da matsayin Najeriya na cibiyar zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin da take ciki.

A wani labarin kuma, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, ya cika alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabensa a shekarar 2015 duk da shakkun da ‘yan adawa ke nunawa.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da yakin neman sake zaben sa a shekakar 2019, karkashin inuwar jam’iyyar APC a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom a ranar Juma’a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel