Allahu Akbar: Fawziya Tataru ta rasu ranar Juma'a, ana shirin daura aurenta a ranar Asabar

Allahu Akbar: Fawziya Tataru ta rasu ranar Juma'a, ana shirin daura aurenta a ranar Asabar

Iyalan gidan Alhaji Abdulkadir Tataru dana Injiniya Salisu Alhaji Boyi sun tsinci kawunansu a cikin tsananin kaduwa da tashin hankali, bisa rasuwar Fawziya Abdukadir Tataru, wacce tun a ranar Juma’a aka gudanar da walimar aurenta da angonta Abduljalal Salisu Boyi.

Cikin kankanin lokaci labarin rasuwar Fawziyya ya karade kafafen sada zumunta na zamani, kasancewarta ma’abociya shafukan sada zumuntar, wacce kuma ta kammala karatunta a jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, tare da kammala bautar kasarta a wannan shekarar ta 2018.

KARANTA WANNAN: Farfado da tattalin arziki na bukatar masana kasuwanci, zamu zabi Atiku/Obi a 2019 - Sarakunan gargajiya

Fawziya Abdukadir Tataru

Fawziya Abdukadir Tataru
Source: Twitter

Babu wanda ya taba kawowa ransa cewa mutuwa zata ziyarci Fawziya Abdulkadir Tataru a wannan gabar ta rayuwarta, musamman yadda ta kasance mace mai girmama na gaba da ita, kuma wacce ta kasance mai kyautata mu’amalarta da jama’ar da take hulda yau da kullum da su –wannan kuwa wata shaida ce da ta samu daga mafi yawan ma’abota kafafen sada zumunta na zamani da suka yi jimamin mutuwarta.

Tun a fari, an shirya daura auren Fawziya da angonta Abduljalal a yau (Asabar), da misalin karfe 11 na safe, a masallacin Juma’a na Gwallaga da ke cikin kwaryar karamar hukumar Bauchi, a jihar Bauchi, sai dai, tun bayan rasuwarta a daren jiya, aka mayar da wannan lokaci da waje ya zamo lokaci da wajen da za a gudanar da Sallar Jana’izarta.

A ranar 8 ga watan Disamba, Fauziyya ta wallafa katin sanarwar daurin aurenta a shafinta na Facebook, inda har ta bukaci daukacin jama'a dasu tayata yin godiya ga Allah akan wannan hanya ta aure da ya zaba mata.

Kadan daga ra'ayoyin ma'abota shafin sada zumunta na Facebook kan mutuwar Fawziya.

1.

2.

3. Wani ma'abocin kafar Facebook, Sada Bn Sulaiman, ya ce:

"Da tuni yau ne daurin aurenta, amma ina! An riga kammala gidanta na qarshe (kabari) a kan gidan amarcinta. Da kanta ta wallafa katin gayyatar daurin auren a shafinta na Facebook.
Haka kullum mutuwa ke bar mana darasi, amma bayan kwana biyu sai mu manta!
Allah Ya jiqan Fauziyya, Ya sa mu cika da imaani."

4.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel