Farfado da tattalin arziki na bukatar masana kasuwanci, zamu zabi Atiku/Obi a 2019 - Sarakunan gargajiya

Farfado da tattalin arziki na bukatar masana kasuwanci, zamu zabi Atiku/Obi a 2019 - Sarakunan gargajiya

- Mr. Peter Obi ya ce babban abunda Nigeria ke bujata yanzu shine babbar tawagar kwararru da zata yi kyakkyawan nazari kan hanyoyin yiwa tattalin arzikin kasar garanbawul

- Obi ya bada tabbacin cewa takarar Atiku/Obi na da cikakken cikakken ilimi kan hanyoyin farfado da tattalin arzikin kasar, samar da ayyukan yi da magance matsalar zaman banza

- A yayin taron masu ruwa da tsakin da Mr Obi ya halarta, sarakunan gargajiya na kasar Aguata, su 13, sun yi mubayi'a ga takarar Atiku/Obi a zaben 2019

Abokin takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Mr. Peter Obi ya ce babban abunda Nigeria ke bujata yanzu shine babbar tawagar kwararru da zata yi kyakkyawan nazari kan hanyoyin yiwa tattalin arzikin kasar garanbawul. Obi ya bayyana hakan hakan a garin Isuofia, a gidan Chief Ozomma Uba, a wani taron masu ruwa da tsaki na al'ummar Aguata.

Obi wanda yace ziyarar tasa ta kasance ne 'bagadatan', kasamcewar yazo ganawa da wani abokinsa ne kawai, ya bada tabbacin cewa takarar Atiku/Obi, ita ce keda cikakken ilimi kan hanyoyin farfado da tattalin arzikin kasar, samar da ayyukan yi da kuma magance matsalar zaman banza, wanda a cewarsa, sune manyan sabubba na faruwar ta'addanci a kasar.

Da yake jawabi a wajen taron, babban manajan kamfanin Pokobros Nig Ltd kuma sanannen dan kasuwa, Chief Paul Okonkwo ya ce zabar Atiku da Obi zai tabbatar da haihuwar sabuwar Nigeria mai cike da tattalin arziki, duba da irin kyawawan kudurorinsu npda kuma sanin makamar farfado da arziki da alkinta ma'adanai.

KARANTA WANNAN: Badakalar WAEC: Dalilin da yasa bamu cafke hadimin Buhari ba - Rundunar 'yan sanda

Mr Peter Obi

Mr Peter Obi
Source: Twitter

A yayin da yake tariyo yadda mulkin Obi ya kasance a lokacin da yake matsayin gwamnan jihar Anambra, Chief Okonkwo ya ce: "Mulkin Obi ne ya farfado da masana'antun jihar da sukayi dogon suma. A matsayinsa na dan kasuwa, muna tattaunawa dashi akai akai, ya fahimci abubuwan da fannin ke bukata kuma ya bayar da goyon bayan sa 100 bisa 1000. Muna da yakinin cewa zai yi fiye da hakan ga Nigeria idan har ya samu nasarar zama mataimakin shugaban kasa."

Abubuwan da suka wakana a taron sun hada da mubayi'ar sarakunan gargajiya 13 na kasar Aguata da suka halarci taron ga takarar Atiku/Obi. Sun kuma yi masa addu'o'i tare da basa tabbacin cewa sarakunan Anambra dama masu son ci gaban kasar zasu zabesu a 2019 don dawo da martabar tattalin arzikin kasar a idon duniya.

Wasu daga cikin manyan masu ruwa da tsaki daga yankin Aguata da suka halarci taron sun hada da: Chief Godwin Okafor, manajan daraktan kamfanin katifa na Winco; Chief Uche Obiakor, Chief Patrick Ifionu2; Chief Emma Nwafor, da dai sauransu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel