Dandalin Kannywood: An samu sabani tsakanin Nafisa Abdullahi da Hadiza Gabon

Dandalin Kannywood: An samu sabani tsakanin Nafisa Abdullahi da Hadiza Gabon

Daya daga cikin fitattun fuskoki a masana'antar shirya fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood watau Nafisa Abdullahi ta tabbatar da samun sabanin da ya auku a tsakanin ta da jaruma Hadiza Gabon a kwanakin baya.

Jarumar dai ta bayyana hakan ne a lokacin da take zantawa da majiyar mu ta BBC kai tsaye a dandalin sadarwar zamani na Facebook a kwanakin baya.

Dandalin Kannywood: An samu sabani tsakanin Nafisa Abdullahi da Hadiza Gabon

Dandalin Kannywood: An samu sabani tsakanin Nafisa Abdullahi da Hadiza Gabon
Source: UGC

KU KARANTA: An kama matashi mai bautar kasa da matar wani

Legit.ng Hausa ta samu cewa duk da dai ba ta amsa tambaya game da dalilin da ya janyo sabani tsakaninsu ba a cikin firar, amma ta ce abu ne da ya faru kusan shekara daya da rabi, kuma ya riga ya wuce.

"Ba ni son sake dauko wannan zancen."

A shekarar 2017 ne fitattun jaruman guda biyu suka yi fada inda wasu rahotanni suka ce har da duka yayin da suke tsakar shirya wani fim.

Nafisa ta ce babu wata dangantaka tsakaninta da Hadiza Gabon, bayan an tambaye ta ko suna kiran juna a waya.

"Ba mu cika haduwa da Hadiza Gabon ba, idan mun hadu muna dan gaisawa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel