'Yan Najeriya 7 da suka yi fice a duniya a 2018

'Yan Najeriya 7 da suka yi fice a duniya a 2018

Allah ya albarkaci yan Najeriya da tarin hikima da fasaha, sun kasance mutane masu kwazo da kokari a kulli yaumin don ganin sun bayar da gudunmawarsu a duniya da kuma rayuwar mayoyansu.

A kullun Lagit.ng na kokarin gano yan Najeriya masu hazaka da kokari a fadiun duniya domin ta sanarwa da jama’a nasarorin da suka samu.

Hakan ya sa muka zakulo maku daga ciki wasu yan Najeriya bakwai da suka shahara bama a gida Najeriya kadai ba harma ga duniya baki daya.

1) Kareem Waris: Ya kansace dan shekara 1 da ya iya zane ya kuma bayar da gudunwa ta hanyar zana hotunan shahararrun yan Najeriya. Ya shahara ne a duniya bayan ya zana wani hoto na shugaban kasa Emmanuel Macron a lokacin da ya ziyarci Najeriya.

2) Ndubisi Ezerioha: Wani dan Najeriya ne da ke da ilimin kera mota kuma shine yak era wata motar carburetted wacce tafi kowace mota sauri a duniya. Shine mammalakin Bisimoto Engineering, kamfanin da ke kera injina ga manyan kamfanonin kera motoci kamar su Honda.

3) Amasa Firdausi: An tauye wa wannan matashiya hakkinta na zama Lauya a ranar 12 ga watan Disamba 2017, duk da cewar ta kammala makarantar lauyoyi, saboda ta sanya hijabi akan hular tan a lauyoyi. Daga baya an yi bikin zamarta cikakkiyar lauya watanni bakwai bayan ta yi yakin neman hakkinta.

4) Elizabeth Bright: Daliba yar Najeriya mai shekara 22 da ke da zama a Ingila wacce ta kafa tarihi bayan an zabe ta a matsayin kansila mai wakiltan Eastbrook da ke Dagenham a kasar Ingila. Bright ta zama mai nasara a ranar 4 ga watan Mayu 2018 bayan zabe da aka yi.

5) Toni Iwobi: Shine dan Najeriya na farko da aka zba a matsayin bakin Sanata a Italy. Yana zaune a kasar Italy tun a shekarar 1970s. Mutumin mai shekaru 62 ya zama sanata bakar fata na farko a Italy a 2018.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Buhari zai dasa sabon gini ne – Tinubu

6) Daliban Whitesands: Daliban makarantun Whitesands hudu sun zamo zakaru na wani rukuni a gidauniyar Conrad Foundation Spirit of Innovation Challenge. Afolabi Williams, Olubusiyi Famobiwo, Menashi Mordi da kuma Osagumwenro Naaman Ugbo, wanda dukkaninsu yan daliban makarantar karamar sakandare ne, sun lashe wani gasa na duniya.

7) Kishin kasa: Wani matashin dan Najeriya ya nuna shi zakara ne ta hanyar kera wani jirgi mai tashi da saukar ungulu wa sojojin Najeriya. Matashin wanda ya fito daga jihar Kaduna ya gabatar da jirgin a jihar Borno domin a gwada.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel