Zaben 2019: Gwamna Masari zai kaddamar da kamfen dinsa a gobe

Zaben 2019: Gwamna Masari zai kaddamar da kamfen dinsa a gobe

- Gwamna Aminu Bello Masari zai kaddamar da kamfen dinsa na sake neman kujerar gwamna a karo na biyu

- Za’a gudanar da gagamin siyasar ne a karamar hukumar Funtua da ke jihar Katsina

- Babban sakataren gwamnatin jihar yace babu makawa Masar zai kai labara saboda ayyukan da gwamnatinsa ta yi a fadin jihar

Gwamna Aminu Bello Masari zai kaddamar da kamfen dinsa na sake neman kujerar gwamna a karo na biyu a karamar hukumar Funtua da ke jihar Katsina.

Shugaban kungiyar kamfen din Masari kuma sakataren gwamnatin jihar, Dr Mustapha Inuwa wadanda ya yi jawabi ga taron manema labarai a jiya Alhamis, 27 ga watan Disamba ya ce tawagar kamfen din za su zagaye dukkanin kananan hukumomi 34 da ke jihar.

Zaben 2019: Gwamna Masari zai kaddamar da kamfen dinsa a gobe

Zaben 2019: Gwamna Masari zai kaddamar da kamfen dinsa a gobe
Source: Facebook

Ya ce a matsayin su na mambobi masu biyayya ga APC, za su bi dukkanin sharuda da ka’idojin kamfen, inda ya kara da cewa nasarorin da gwamnatin Masari ta samu a kowani bangare na jihar ya isa ya bayar da tabbacin cewa zai yi nasarar yin tazarce.

A cewarsa, za’a kaddamar da dukkaninayyukan da aka kammala a dukka wuraren da za su ziyarta.

KU KARANTA KUMA: Shehu Sani yi martani bayan ikirarin cewa iyalan Buhari na da hannun jari a kamfanoni 2

Ya kuma kara da cewar za kuma su karbi sabbin mambobin siyasa da suka sauya sheka daga sauran jam’iyyun siyasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel