Yan Boko Haram sun kona makarantun jihar Yobe uku cikin kwanaki biyu

Yan Boko Haram sun kona makarantun jihar Yobe uku cikin kwanaki biyu

Wasu yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram sun kona makarantun firamare biyu, da barikin yan sandan daya a jihar Yobe cikin kwanaki biyu kacal.

An kai hari wadannan makarantar firamaren Kuka-reta, makarantan firamaren Katarko da makarantan Ngaurawa inda dimbin yan gudun hijra ke karatu ne a ranan 24 da 26 ga watan Disamba 2018.

Hakimin garin Kuka-reta, Lawani Babagana, makarantan Kuka-reta wacce ake fadadawa cewa yaran yan gudun hijra ke samun damar zuwa tun lokacin da yaki ya koresu daga muhallansu.

"Bamu san yadda zamuyi idan dalibai suka koma makaranta ba." Yace

KU KARANTA: Yadda muka kashe Alex Badeh, faifan bidiyon daya daga cikin makasan

Wani mazauni, Alhaji Muhammad Goni, ya bayyana cewa a shekarar 2014, yan ta'addan sun kona makarantan amma gwamnatin jihar sun gyara a 2015.

Yace: "Abin takaici, sun sake rusa makarantan. Daruruwan dalibai na halartan makarantan, har da yaran da suka bar sansanin IDP kwanan nan"

Wadannan hare-haren na bamu tsoro kuma ya tilasta da dama daga cikinmu barin muhallansu saboda bamu san abinda ke cikin ran wadannan yaran ba."

"Wajibi ne mu gudu daga muhallanmu saboda Sojoji ba zasu iya karemu ba. Sune mutanen farko dake arcewa duk lokacin da aka kawo hari."

A bangare guda, mun kawo muku rahoton cewa yan Boko Haram sun kai mumunan hari garin Baga har sun kai ga kwace garin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel