Da dumin sa: 'Yan Boko Haram sun kwace karamar hukuma sukutum a Borno

Da dumin sa: 'Yan Boko Haram sun kwace karamar hukuma sukutum a Borno

Rahotannin da muke samu daga garin Baga da ke jihar Barno a arewa maso gabashin Najeriya suna nuni ne da cewa mayakan 'yan ta'addan Boko Haram sun shiga garin inda suka kara da sojojin Najeriya kafin daga bisani su fatattake su.

Daya daga cikin wadanda artabun ya faru akan idon sa ya shaida wa majiyar mu cewa mayakan na Boko Haram da suka ce daga bangaren Mamman Nur ne sun afkawa wani babban sansanin soji da ke gefen ruwa a garin na Baga.

Da dumin sa: 'Yan Boko Haram sun kwace karamar hukuma sukutum a Borno
Da dumin sa: 'Yan Boko Haram sun kwace karamar hukuma sukutum a Borno
Asali: Getty Images

KU KARANTA: An yi wa Saraki ihu 'barawo' a Kwara

Legit.ng Hausa ta samu cewa mutumin ya kara da cewa da misalin karfe 4 na yamma ne mazauna garin suka fara jin karar harbe-harben bindigu da sauran makamai inda ake musayar wuta tsakanin 'yan ta'addan da dakarun sojoji har kusan karfe takwas na dare.

Majiyar ta mu har ila yau ta bayyana mana cewa daga baya mayakan sun shiga garin na Baga bayan wasu daga cikinsu sun yi wa sansanin sojojin kawanya a daidai lokacin da sojojin da ke cikin garin na Baga suka tsere zuwa Munguno.

Ya bayyana cewa mayakan sun kafa tutarsu a babban masallacin Juma'a na garin Baga, kuma 'yan bindigan ne ma suka ja sallar Asuba.

Sai dai rundunar sojin Najeriya dai ta sanar cewa mayakan Boko Haram sun kai hari shelkwatar dakarun gamayya na kasashen yankin tafkin Chadi ne da ke Baga a jiya Laraba.

Ta ce dakarunta sun yi fada kan jiki kan karfi don korar mayakan Boko haram din, kuma daya daga cikin sojojin ya rasa ransa a yayin fadan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel