Mutane 10 sun mutu, 5 sun jikkata a sabon harin da aka kai Plateau

Mutane 10 sun mutu, 5 sun jikkata a sabon harin da aka kai Plateau

- Mutane goma sun mutu yayinda wasu biyar suka jikkata a wasu sabbin hare-hare biyu da yan bindiga suka gudanar a karamar hukumar Barki Ladi da ke jihar Plateau

- An kashe mutane biyar a daren ranar Laraba, 26 ga watan Disamba yayinda suke bikin Kirsimeti a garin Rawuwu da ke karamar hukumar

- Sannan kuma sauran biyar din sun mutu bayan yan bindiga sun far masu a wani otel da ke Gwol washegarin ranar

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa an tabbatar da mutuwar mutane goma yayinda wasu biyar suka jikkata a wasu sabbin hare-hare biyu da yan bindiga suka gudanar a karamar hukumar Barki Ladi da ke jihar Plateau.

Sabbin hare-haren na zuwa ne kasa da mako guda bayan an tura tawaga na musamman domin dawo da zaman lafiya a jihar bayan kwashe mutane 200 daga sansanin gudun hijira a Jos zuwa kauyukansu wanda suka bari a baya sakamakon yawan hare-hare day an bindiga ke kaiwa.

Mutane 10 sun mutu, 5 sun jikkata a sabon harin da aka kai Plateau
Mutane 10 sun mutu, 5 sun jikkata a sabon harin da aka kai Plateau
Asali: Depositphotos

Jaridar Punch ta ruwaito cewa an kashe mutane biyar a daren ranar Laraba, 26 ga watan Disamba yayinda suke bikin Kirsimeti a garin Rawuwu da ke karamar muhumar yayinda aka kashe biyar bayan yan bindiga sun far masu a wani otel da ke Gwol washegarin ranar.

KU KARANTA KUMA: 2019: Kungiya ta fara bi gida-gida don wayar da kan mutane a mahaifar Buhari

Kakakin yan sandan jihar, DSP Mathias Terna yace zai halarci wani ganawa na tsaro lokacin da aka kira shi akan lamarin.

Amma wani jigo a garin, Mista Francis Chong ya tabbatar da sabon harin da aka kaiwa mutanen a ranar Alhamis 27 ga watan Disamba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel