Yanzu-yanzu: Yadda muka kashe Alex Badeh, faifan bidiyon daya daga cikin makasan

Yanzu-yanzu: Yadda muka kashe Alex Badeh, faifan bidiyon daya daga cikin makasan

Mun kawo muku rahoton cewa jami'an hukumar yan sandan Najeriya sun cika hannu da wadanda ake zargi da kisan tsohon babban hafsan sojin Najeriya, Air Chief Marshal Alex Sabundu Badeh a makon da ya gabata.

Jawabin majiya mai karfin ya bayyana cewa zasu baja kolin makasan a ranan Alhamis a hedkwatan hukumar dake Abuja amma suka fasa hakan bisa ga wasu dalilai.

A yau, rundunar 'yan sanda ta kasa ta bayyana cewar ta daga bajakolin wadanda suka kashe tsohon shugaban rundunar askarawan soji ta kasa, Alex Badeh, ga manema labarai.

KU KARANTA: Buhari yayi ba’a ga Saraki, yace zai raba Kwara da dukkanin masu laifi kafin 2019

Da yake bayyana nasarar kama wadanda ake zargin, DCP Jimoh Moshood, kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, ya ce an kama mutane 5 dake da hannu a kisan Badeh.

Moshood ya kara da cewa, rundunar 'yan sanda ta fasa gabatar da masu laifin ne saboda gudun kar ragowar dake da hannu a aikata laifin kisan su tsere.

Kafin sakin wannan jawabi, daya daga cikin wadanda suka aikata wannan aika-aika yayi magana da manema labarai a wannan faifan bidiyon inda yace:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel