Fadar shugaban kasa ga 'yan Nigeria: Kuyi hattara da jam'iyyar makaryata ta PDP

Fadar shugaban kasa ga 'yan Nigeria: Kuyi hattara da jam'iyyar makaryata ta PDP

- Fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gargadi 'yan Nigeria da suyi hattara da jam'iyyun adawa, musamman ma jam'iyyar PDP

- Haka zalika ta yi fatali da zargin PDP na cewar gwamnatin Buhari ta handame $322m da aka kwato a baya bayan nan daga iyalan Abacha

- Garba Shehu ya bayyana cewa $322m da aka kwato, anyi amfani da su wajen bullo da shiri nan na tallafawa marasa karfi, mai suna Conditional Cash Transfer (CCT)

Fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gargadi 'yan Nigeria da suyi hattara da jam'iyyun adawa, musamman ma jam'iyyar PDP, don karsu bige zaben jam'iyyar da bata damu da cin hanci da rashawa ba.

Malam Garba Shehu, babban hadimin shugaban kasa Muhmmadu Buhari ta fuskar kafofin sadarwa da hulda da jama'a, ya bada wannan shawarar a lokacin da yake mayara da martani kan wani zargi da jam'iyyar PDP take yiwa gwamnatin shugaba Buhari.

Shehu, a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Abuja a ranar Laraba, ya ce PDP na zargin gwamnatin Buhari ne kawai saboda son karkatar da zukatan 'yan Nigeria daa ganin barnar da tayi a cikin shekaru 16.

KARANTA WANNAN: Har in mutu, Buhari zai ci gaba da kirana 'Sir' - Obasanjo ya maida martani

Fadar shugaban kasa ga 'yan Nigeria: Kuyi hattara da jam'iyyar makaryata ta PDP

Fadar shugaban kasa ga 'yan Nigeria: Kuyi hattara da jam'iyyar makaryata ta PDP
Source: Depositphotos

A cewarsa, jam'iyyar PDP na ci gaba da yada karairayi akan gwamnatin Buhari akan wasu gurbatattun hasashe da take yi na cewar gwamnatin ta gaza wajen yaki da cin hanci da rashawa, yana mai cewa wannan yunkuri ne kawai na gogawa jam'iyyar kashin kaji don 'yan Nigeria su tsaneta.

Ya ce: "Wannan karairayin nasu ya ta'allaka ne kawai wajen nunawa 'yan Nigeria cewa kowanne gauta ja ne. Suna ganin cewa idan suka yi hakan, 'yan Nigeria zasu iya yafe masu zunuban da suka aikata a baya. Wannan kuwa babban kuskure ne da suka yi.

"Zai zama abun shirme ace wai jam'iyyar ce zata rinka shelantawa 'yan Nigeria cewa shugaba Buhari na rashawa, kamar yadda suke yada jita jitar cewa gwamnatin ta handame $322m da aka kwato a baya bayan nan daga iyalan Abacha. Wannan kowa yasan wannan karya ce tsagoranta."

Garba Shehu ya bayyana cewa $322m da aka kwato, anyi amfani da su wajen bullo da shiri nan na tallafawa marasa karfi, mai suna Conditional Cash Transfer (CCT), wanda ake baiwa marasa karfi tallafin N5,000 a kowanne wata, kuma akalla talakawa 300,000 ne ke cin gajiyar shirin.

"Don haka fadar shugaban kasa na shawartar 'yan Nigeria da su yi taka tsantsan da kalaman jam'iyyar PDP, kar su bari a yaudaresu don zabar jam'iyyar da ta dauki cin hanci da rashawa ba abakin komai ba," a cewarsa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel