Kabari kusa: An gano karin ciwalwatan da zukar shisha ke jazawa a jikin dan adam

Kabari kusa: An gano karin ciwalwatan da zukar shisha ke jazawa a jikin dan adam

Wata likita mai suna Dakta Moji Fasiku ta gargadi matasa game da illolin da ke tattare da sabuwar dabi’ar zukar hayaki ta shisha.

A wani taron wayar da kan jama’a game da cutar dajin hanta wanda aka gudanar a jiya Alhamis, likitar ta ce ta san shisha ya zama ruwan dare a tsakanin matasa a matsayin wata hanya ta jin dadi, inda ake jan hankalinsu da hayaki mai dandano daban daban.

Kabari kusa: An gano karin ciwalwatan da zukar shisha ke jazawa a jikin dan adam
Kabari kusa: An gano karin ciwalwatan da zukar shisha ke jazawa a jikin dan adam
Asali: UGC

KU KARANTA: Atiku ya kada Buhari a wani zaben gwaji

Legit.ng Hausa ta samu haka zalika cewa likitar ta ce abunda ke cikin tabar sigari shi ake karawa dandano mai dadi a sayar da shi a matsayin dandanon shisha, a don haka ya na dauke da sinadaran da ke cikin sigari wadanda ke haifar da illa.

Ta kara da cewa, illar abun ba yanzu ake gani ba sai lokacin da tsufa ya nufo mutum.

Likitar ta kuma ce, banda shan sigari da shisha, shakar hayakin girkin itace shi ma ka iya haifar da cutar dajin huhu.

A don haka ne ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta saukaka farashin kalanzir da iskar gas domin a ceto matan Nijeriya daga illar da ke tattare da girkin itace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel