Yanzu-yanzu: An damke wadanda suka kashe Alex Badeh

Yanzu-yanzu: An damke wadanda suka kashe Alex Badeh

Labarain da ke shigo mana da dumi-dumi na nuna cewa jami'an hukumar yan sandan Najeriya sun cika hannu da wadanda ake zargi da kisan tsohon babban hafsan sojin Najeriya, Air Chief Marshal Alex Sabundu Badeh a makon da ya gabata.

Hukumar yan sandan Najeriya zata bayyana wadanda aka kama ranan Alhamis, 27 ga watan Disamba 2018 a hedkwatan hukumar dake birnin tarayya Abuja.

Majiya mai karfi daga hukumar yace: "Mun samu nasara a wannan bincike kuma mun damke wasu kuma za'a bayyanasu ranan Alhamis."

An kashe tsohon janar Badeh da yammacin ranan Talata, 18 ga watan Disamba 2018 yayinda yake dawowa daga gonarsa daga karamar hukumar Keffi dake jihar Nasarawa.

An budewa motarsa kirar Toyota Tundra wuta inda ya mutu a take. Alex Badeh kadai ya mutu cikin mutane uku dake cikin motar. hakan ya sanya ana zargin cewa shi akayi bukatan kashewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel