Hauka-maganinka-Allah: Wata mata ta shiryawa dakwalen kajin ta kayatacceb bikin aure

Hauka-maganinka-Allah: Wata mata ta shiryawa dakwalen kajin ta kayatacceb bikin aure

- Wata mata mai suna Erin ta yada a shafin ta na dandalin sadarwar zamani hotunan wasu kajin ta da ta yiwa aure

- Erin a jikin hotunan da ta yada, ta kuma bada labarin yadda kazar da zakaran suka hadu kuma har suka yi aure

Aure na daya daga cikin labarai mafiya dadi da jinsin mutane kan ji dadin su tare kuma da tattauna shirye-shiryen su, musamman ma idan ya hada da masoya masu son junan su tsantsa.

Sai dai a wannan labarin da muke dauke da shi, a iya cewa maganar auren ta dauki sabon salo domin kuwa a maimakon mutane kamar yadda aka saba, wata dakwalwar kaza ce aka daurawa aure da zakara.

Hauka-maganinka-Allah: Wata mata ta shiryawa dakwalen kajin ta kayatacceb bikin aure

Hauka-maganinka-Allah: Wata mata ta shiryawa dakwalen kajin ta kayatacceb bikin aure
Source: UGC

KU KARANTA: Makarantar kwana ta kori dalibai 8 da cikin shege

Legit.ng Hausa ta samu cewa matar da ta dauki nauyin shagulgulan bikin ta bayyana irin yadda ta fahimci kajin na son junan su wanda har hakan ya jaza ta yi tunanin daura masu auren domin cikar burin su.

Matar ta kara da cewa a lokutta da dama dai ita da dukkan mazauna unguwar su, sun fahimci cewa a kulluma sukan ga kajin a tare suna kiwo kuma har ma a wani lokaci da zakarar ya samu hadari kazar ta damu sosai.

Ga dai wasu daga cikin hotunan:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel