Allah-daya-gari banban: Ku karanta labarin wani garin da rana ke kwana 65 bata fito ba

Allah-daya-gari banban: Ku karanta labarin wani garin da rana ke kwana 65 bata fito ba

Kamar dai yadda Hausawa kan ce wai Allah daya amma gari ban ban, to yau ma dai gamu dauke da labarin wani gari dake a wata jiha daga jahohin kasar Amurka mai cike da abun al'ajabi da ban mamaki musamman a garemu 'yan Nahiyar Afrika.

Garin dai mai suna Barrow a da kafin a canza masa suna zuwa Utqiaġvik yana da wasu siffofi na musamman domin kuwa a duk shekara akan yi kwanaki 65 ba tare da rana ta fito ba.

Allah-daya-gari banban: Ku karanta labarin wani garin da rana ke kwana 65 bata fito ba

Allah-daya-gari banban: Ku karanta labarin wani garin da rana ke kwana 65 bata fito ba
Source: Facebook

Legit.ng Hausa ta samu cewa garin na Utqiaġvik idan rana ta fadi a tsakiyar watan Nuwamba to ba ta sake fitowa har sai 23 ga watan Janairu wanda yake daidai da kwanaki 65.

Garin dai kamar yadda muka samu yana a kusa ne da karshen duniya a wani zango da ake kira Arctic Circle Arctic Circle dake da tsaanin sanyi.

Duk da dai ba kowa ne ke iya zama a garin ba, amma jama'ar garin a iya cewa sun saba da hakan domin kuwa idan har lokacin ya gabato su kanyi kykkyawan shirin tarbar yanayin har zuwa lokacin da zai wuce.

Ga dai wasu daga cikin hotunan kamar yadda wata kafar labarai ta kasar Amurkar ta wallafa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel