Fa’idojin da ke tattare da amfani da namjin goro ga lafiyar jiki

Fa’idojin da ke tattare da amfani da namjin goro ga lafiyar jiki

Namijin goro wanda a ka fi sani da 'garcinia kola' yawanci a fi samunsa a kasashen Afirka, kuma shekaru aru-aru a na amfani da shi don yin magani a al'adun Afirka.

Ya na dauke da sinadarin 'dimeric flavonoid' wanda a ke ganin ya na yin magunguna da dama.

A yau za mu fada muku manya-manyan amfanin namijin goro. A na noman wannan dan itace ne a kasashen Najeriya, Kamaru, Ghana, Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, Benin, Kwadebuwa, Gabon, Saliyo, Laberiya, da kuma Sanegal.

Fa’idojin da ke tattare da amfani da namjin goro ga lafiyar jiki

Fa’idojin da ke tattare da amfani da namjin goro ga lafiyar jiki
Source: UGC

Mutanen Afirka sun dade da gano amfanin namijin goro ga lafiya. A tarihance, likitoci a Afirka sun yi imani cewa, namijin goro na da sinadarin yakar kaska, da yashe ciki, da kuma yakar kananan kwayoyin cuta.

1. Likitoci na amfani da shi don maganin tari da cututtukan makogwaro, da bututun iska, da ciwon kai ko sanyin kirji, da kuma ciwon ciki.

2. Tsarin maganin gargajiya na Afirka ya nuna masu matsalar hanta ka iya tauna namijin goro.

3. Namijin goro na taimaka wa wajen maganin dukkan nau'i na tari, a na kuma amfani da shi wajen maganin sanyi. Yawanci kuma ya fi amfani wajen kakkabe mashako, da tari, da toshewar hanci, da kuma majina.

4. Namijin goro na taimakawa wajen yakar miyagun cututtuka kamar Ebola, ya na kuam dauke da sinadaran yakar dadewar fata da sauransu.

KU KARANTA KUMA: Dan takarar shugaban kasa a APC ya sauya sheka zuwa PDP

5. Ya na kara karfin kwaranyar jini ga mutanen da ke da matsala da bututun da ke dauko jini daga zuciya.

6. Namijin Goro na taimaka wa garkuwar jiki,domin binciken kimayya na musamman ya tabbatar da cewa, yawan amfani da shi na ba da kariya ga garkuwar jikin dan adam.

7. Har ila yau Namijin goro na warkar da ciwon gwiwa wajen rage mata radadi sosai yana kuma amfani wajen jin yunwa sannan ya na sa jin kishirwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel