Amfanin Gishiri guda 5 da ya kamata kowa ya sani

Amfanin Gishiri guda 5 da ya kamata kowa ya sani

Gishiri na da amfani da daba baya ga zubawa a cikin abinci, mutane da yawa na zaton amfanin gishiri shi ne kawai a zuba a cikin miya, amma ina, amfaninsa ya fi ga haka.

Amfanin Gishiri guda 5 da ya kamata kowa ya sani

Amfanin Gishiri guda 5 da ya kamata kowa ya sani
Source: UGC

Ga wasu daga cikin amfanin sa:

1. Ana amfani da gishiri wajen kankare kyandir daga wuri, mutun zai jika Kyandir din kna tsawon awa biyu ko uku, to da zaran an kunna shi, yana ci, ko da zai diga a waje, ba zai kama ba. Da zaran mutun ya murje shi, zai fita, tamkar babu abunda ya taba diga a wajen.

2. Idan kina kokwanto akan lafiyar kwai ko ya lalace ko yana da kyau, sai ki zuba gishirin ki cikin karamin cokali biyu a ruwa, ki kada, ki zuba kwan a ciki, idan yana da kyau za ki ga kwan ya yiwo sama yana yawo, idan kuma ya lalace ne kuma za ki ga ya yi kasa.

3. Ana amfani da ruwa mai dumi wajen kurkure baki a lokacin da mutun ke fama da ciwon hakori, kuma da yardar Allah sai yayi sauki.

KU KARANTA KUMA: Dan takarar shugaban kasa a APC ya sauya sheka zuwa PDP

4. Ana kuma amfani da gishitri a yayinda zuma ya harbi mutun, sai sai yayi gaggawan zuba ruwan gishiri a wajen, hakan zai rage radadin harbin zumar, kuma wajen ba zai tashi ya yi ja ba.

5. Idan kina da madarar ruwa kuma tana saurin lalacewa, sai ki zuba gishiri dan kadan a ciki ki jijjiga ki rufe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel