Da kanwar Kanal Sakaba nayi magana ba uwargidansa ba - Atiku

Da kanwar Kanal Sakaba nayi magana ba uwargidansa ba - Atiku

- Atiku Abubakar ya janye labarinsa na farko na yin magana da uwargidan Laftanal Kanal Sakaba, wanda Boko Haram suka kashe a Matele

- Yace akasi aka samu wajen sadarwa domin da yar’uwar marigayin Maryam yayi magana ba uwargidan marigayin ba

- Ya kuma bayar da hakuri akan wannan akasi da aka samu

Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party, a ranar Litinin, 24 ga watan Disamba ya janye labarinsa na farko na yin Magana da uwargidan Laftanal Kanal Sakaba, wanda Boko Haram suka kashe a Matele a watan da ya gabata.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa a yanzu yace yayi Magana ne da yar’uwar marigayin sojan, Marym, dan takarar na PDP yace akasi aka samu day a yada a yanar gizo cewa yayi Magana da Seun, matar Sakaba.

Da kanwar Kanal Sakaba nayi magana ba uwargidansa ba - Atiku
Da kanwar Kanal Sakaba nayi magana ba uwargidansa ba - Atiku
Asali: Facebook

Sai dai matar ta karyata amsa wani kiran waya daga Atiku sannan tayi al’ajabin dalilin da yasa dan siyasar mai shekaru 72 yayi karya. Yanzu Abubakar ya nadi murya kai tsaye sannan ya bayar da hakuri akan akasi d aka samu wajen sadarwa.

Mun kawo muku rahoton cewa rundunar sojin ajeriya a ranar Laraba, 28 ga watan Nuwamba ta kai ziyarar jaje da ta’aziyya ga wata mata mai suna II Sakaba, matar jarumin sojan da ya mutu, Lieutenant Colonel Ibrahim Sakaba.

KU KARANTA KUMA: Atiku makaryaci ne, bai kirani a waya ba - Matar Kanal Sakaba ta karyata ikirarin dan takaran

Legit.ng ta tattaro cewa rundunar ta bayyana hakan a shafinta na Twitter a ranar Laraba, 28 ga watan Nuwamba, cewa tawagar rundunar karkashin jagorancin Birgediya Janar SI Igbinomwanhia.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel