Atiku makaryaci ne, bai kirani a waya ba - Matar Kanal Sakaba ta karyata ikirarin dan takaran

Atiku makaryaci ne, bai kirani a waya ba - Matar Kanal Sakaba ta karyata ikirarin dan takaran

Uwargidan marigayi Laftanan Kanal Ibrahim Sakana, daya daga cikin jaruman sojoji 44 da suka rasa rayukansu a harin yan Boko Haram suk kai barinin 157 Task Force Battalion da ke Metele, jihar Borno ta musanta ikirarin Alhaji Atiku Abubakar.

Uwargidan marigayin, Mrs Seun Sakaba, ta siffanta dan takaran kujeran shugaban kasa, Atiku Abubakar, a matsayin makaryaci kan jawabin da ya saki cewa ya kirata a wayan taroho domin yi mata jaje kan mutuwan mijinta.

A ranar Lahadi, Atiku ya bayyana cewa: "A wannan bikin Chrismetin, ina kira ga dukkan yan Najeriya da su yiwa jaruman sojin da suka mutu a faggen yaki addu'a. Na samu daman magana da uwargidan Lt Kanal Ibrahim sakaba kuma irin kaddaran da ta dauki ya bani mamaki."

KU KARANTA:Yunkurin kawo karshen Saraki: Yan jam'iyyar PDP 5000 sun koma APC a jihar Kwara

Yayinda tattaunawa da uwargidan marigayin tayi da jaridar PUNCH, Seun Sakaba ta bayyana cewa bata taba amsa kiran tsohon mataimakin shugaban kasan ba. Ta ce abinda ya bata mamaki babban mutum ya dinga karya.

Tace: "Menene na yin karya? Ni ban samu kira da wajen Atiku ba,"

Mun kawo muku rahoton cewa rundunar sojin ajeriya a ranar Laraba, 28 ga watan Nuwamba ta kai ziyarar jaje da ta’aziyya ga wata mata mai suna II Sakaba, matar jarumin sojan da ya mutu, Lieutenant Colonel Ibrahim Sakaba.

Legit.ng ta tattaro cewa rundunar ta bayyana hakan a shafinta na Twitter a ranar Laraba, 28 ga watan Nuwamba, cewa tawagar rundunar karkashin jagorancin Birgediya Janar SI Igbinomwanhia.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel