Bana tsoron Buhari, Allah kadai nake tsoro – Gwamna Amosun

Bana tsoron Buhari, Allah kadai nake tsoro – Gwamna Amosun

Gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun ya karyata rahoton kafofin watsa labarai da ke cewa shi yace yana tsoron Allah da Buhari. A cewar gwamnan an juya kalaman nasa ne domin shi Allah kadai yake tsoro ba mutun dan Adam kamar shi ba.

Gwamna Ibikunle Amosun na jihar Ogun yayi watsi da rahoton kafofin watsa labarai da suke kawo inda yake cewa yana tsoron Allah daShugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Amosun yayinda yake kari haske akan lamarin a ranar Asabar, 22 ga watan Disamba ya bayyana cewa babu gaskiya a rahoton.

Legit.ng ta tattaro cewa ya bayyana a lokacin taron Kirisimeti da gwamnatin jihar ta shirya a Abeokuta, cewa baya tsoron shugaba Buhari kamar yadda aka rahoto.

Bana tsoron Buhari, Allah kadai nake tsoro – Gwamna Amosun
Bana tsoron Buhari, Allah kadai nake tsoro – Gwamna Amosun
Asali: Depositphotos

Yayinda yake martani akan rahoton kafofin watsa labarai, Amosun yace ya shiga alhini a lokacin da ya karanta shafukan jaridu a ranar Asabar, 22 ga watan Disamba, cewa yana tsoron Allah da Buhari.

KU KARANTA KUMA: Ta kare ma Najeriya idan har Buhari ya kara wasu shekaru 4 anan gaba – Peter Obi

Yace: “Kun san wannan lokaci namu a matsayin yan siyasa, wani lokaci ne day an siyasa za su kira baki da bulu.

“Jiya (Juma’a), na gudanar da wani taro tare da mutanenmu, sannan yadda na fa shine cewar, na taso inda ake mun nuni ga tsoron Allah.

“Amma sai na gani a jaridu a safen nan (Asabar) cewa Amosun yace yana tsoron Allah da Buhari.

“A’a, Allah kadai nake tsoro, sarki guda dake raye, wanda idan yace abu babu mai iya chanjawa. Wannan ne Allah daya da nake tsoro.

“Tabbass ina ganin girman shugaba Buhari. Ina kaunar shi shima kuma yana kauna na. Na san shi, yana tsoron Allah saboda daga Allah yake. Baya rokon a mutunta shi, ya aikata ne kuma ya samu. Don haka Allah kadai nake tsoro.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel