Mahaifin Nura Husaini dan wasan Hausa da ya zagi Sheikh Gumi ya nemi gafara (Bidiyo)

Mahaifin Nura Husaini dan wasan Hausa da ya zagi Sheikh Gumi ya nemi gafara (Bidiyo)

Mahaifin fitaccen dan wasan Hausan nan Nura Husaini da a kwanan baya yayi wani dan karamin bidiyo yana kalubalantar Sheikh Ahmad Gumi game da wasu wa'azojin sa da yake yi musamman ma na caccaka ga gwamnatin Shugaba Buhari yayi tattaki har masallacin Sultan Bello a Kaduna don nemar wa dan nasa afuwa.

Shi dai Jarumin fina-finan na Hausa, Nura Husaini yayi kaurin suna wajen nunawa Shugaba Buhari soyayya inda harma yake daya daga cikin jagororin kungiyar 'yan fim din Hausa dake goyon bayan shugaban kasar.

Mahaifin Nura Husaini dan wasan Hausa da ya zagi Sheikh Gumi ya nemi gafara (Bidiyo)

Mahaifin Nura Husaini dan wasan Hausa da ya zagi Sheikh Gumi ya nemi gafara (Bidiyo)
Source: Twitter

KU KARANTA: Buhari mutumin kirki ne - Fayose

Legit.ng Hausa ta samu cewa a cikin wani dan karamin bidiyon da aka wallafa a shafin shehin malamin na dandalin sada zumunta na Fecebook mai taken "NEMAN AFUWAR MAHAIFIN NURA HUSAINI GA DAKTA AHMAD GUMI", an ga mahaifin na Nura Husaini cike da nadama a gaban malamin.

Haka ma dai daga karshe Malam Gumi ya yafewa jarumin sannan kuma ya bukaci dukkan almajiran sa da sauran masoyan sa da su yafe masa sannan kuma su guji mayar masa da martani ko zagi.

Ga dai bidiyon nan:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel