An kashe wani magidanci mai ’ya’ya 12 kan itacen girki a Kazaure

An kashe wani magidanci mai ’ya’ya 12 kan itacen girki a Kazaure

Wasu mutane da ake zargin masu satar itacen girki ne sun hallaka wani magidanci mai ’ya’ya goma sha biyu a gonarsa da ke kusa da Makarantar Informatics a garin Kazaure, Jihar Jigawa, inda daga baya suka kone gawar da sankacen kara.

Magidancin mai suna Alhaji Mu’awiyya Gaguli mai kimanin shekara 55 ya tafi gona a ranar Juma’ar da ta gabata domin fakon masu sace masa itace a gonar amma bai dawo ba, kuma sai ranar Lahadi aka gano gawarsa a gonar ta fara zagwanyewa.

Kawun marigayin Malam Sabi’u Shu’aibu da ke Unguwar Kantudu a Kazaure ya bayyana cewa marigayinya hadu da ajalinsa ne a lokacin da ya je gonarsa saboda barayi sun dame shi da yawan satar itace a gonar.

An kashe wani magidanci mai ’ya’ya 12 kan itacen girki a Kazaure

An kashe wani magidanci mai ’ya’ya 12 kan itacen girki a Kazaure
Source: Depositphotos

Ya ce ya je gonar ce da niyyar kama wadanda suke sata itacen a ranar Juma’ar da ta gabata, amma har dare bai dawo ba, shi ne matarsa ta zo ta fada a cikin daren suka je gonar ba su same shi ba, amma sun ga jallon ruwansa da buhunsa. Ya ce washegari sun sake komawa gonar suka sake dubawa amma ba su ganshi ba.

KU KARANTA KUMA: Disamba 22: Buhari ya jagoranci taron kungiyar ECOWAS a Abuja

Ya ce wani yaro ne ya zo kusa da gonarsa ya ga gawar shi ne aka sanar da su suna suka je suka gan shi akwai alamun duka a kansa amma babu alamar yanka ko fasa cikinsa da jama’a suka yadawa.

Daga karshe yace a yanzu haka yan sanda suna ta kokarin gano wadanda ke da hannu a lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel