Rikicin Zamfara: Wani shehin Malami Islama ya fadawa Buhari gaskiya

Rikicin Zamfara: Wani shehin Malami Islama ya fadawa Buhari gaskiya

Jagoran darikar Qadiriyya a Nahiyar Afrika, Sheikh Karibullah Kabara ya bukaci shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari da ya gaggauta sake tura dakarun sojoji a jihar Zamfara da ke fama da matsalar tsaro da tashe-tashen hankula.

Sheikh Karibullah Kabara yayi wannan kiran ne a ranar Asabar lokacin da yake jawabi a wurin taron Maulidi na tunawa da shugaban Darikar ta Qadiriyya Sheikh Abdulkadir Jilani karo na 68 a garin Kano.

Rikicin Zamfara: Wani shehin Malami Islama ya fadawa Buhari gaskiya
Rikicin Zamfara: Wani shehin Malami Islama ya fadawa Buhari gaskiya
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kwankwaso ya fara gangamin korar Ganduje a Kano

Shehin Malamin dai ya nuna matukar bacin ran sa da kuma damuwa a game da yadda yace wasu 'yan tsiraru ke gallazawa al'umma a jihar yayin da ita kuma gwamnati tayi burus da lamarin.

A wani labarin kuma, Wani mai maganin gargajiya da kan yi shigar burtu yayi mutane fashi da makami ya gamu da gamon shi yayin da ya shiga hannun jami'an 'yan sandan Najeriya.

Mai maganin gargajiyar dai mai suna Abdullahi Mudi, kamar yadda muka samu ya shiga hannun 'yan sandan ne tare da abokin tafka ta'asar sa mai suna Christopher Illia a wurare daban-daban a garin Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel