Tsuntsun da ya ja ruwa: Wasu 'yan Yahoo Yahoo guda 2 sun gamu da fushin kotu

Tsuntsun da ya ja ruwa: Wasu 'yan Yahoo Yahoo guda 2 sun gamu da fushin kotu

- Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta samu nasara kan karar da ta kai Fabulous Peter da Osahun O. Aiseosa (wanda aka fi sani da) Wesley Jackson

- An cafke mutanen biyu ne bayan kwararan bayanai da aka samu kansu, dangane da zargin da ake masu na damfarar mutane ta hanyar yanar gizo

- Mai shari Senchi ya yanke masu hukuncin watanni 12 a gidan kurkuku ko kuma su biya fansar N1,000,000

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta samu nasara kan karar da ta kai Fabulous Peter da Osahun O. Aiseosa (wanda aka fi sani da) Wesley Jackson, a wata babbar kotun birnin tarayya Abuja da ke da zama a Jabi.

An cafke mutanen biyu ne bayan kwararan bayanai da aka samu kansu, danga da zargin da ake masu na yadda suke gudanar da rayuwarsu, da kuma yadda suke samun kudaden kashewa.

Rahotanni sun bayyana cewa sun samu matsugunni ne a gidan wani mutumi mai suna Aleri E.B, da ke da zama a gida mai lamba 4, rukunin gidaje na River Park, kan hanyar zuwa filin jirgin sama na Abuja.

KARANTA WANNAN: 'Union Bank' ya ce shine mamallakin N1bn da EFCC ta cafke a filin jirgin sama na Enugu

Tsuntsun da ya ja ruwa: Wasu 'yan Yahoo Yahoo guda 2 sun gamu da fushin kotu

Tsuntsun da ya ja ruwa: Wasu 'yan Yahoo Yahoo guda 2 sun gamu da fushin kotu
Source: UGC

Rahotannin sun bayyana cewa wandanda aka yankewa hukuncin, sun boye sunayensu da adireshinsu na ainihi, inda suke amfani da kwamfuta, wayar hannu da kuma kafar yanar gizo, wajen tura sakwannin 'Email' don damfarar jama'a

A cikin watan Yunin 2018 a Abuja, an zargi Aiesosa da damfarar wata yar Amurka, Dian Mary $15,000, wanda yayi dai dai da N5,400,000m, ta hanyar tura masa kudaden a wani asusun bankin Trust Bank, mai lambar asusu 0167955239.

Laifin da suka aikata ya ci karo da sashe na 320(a) na dokar aikata laifuka, a kundin tsarin Abuja 1990, kuma ana yin hukuncinsa karkashin sashe na 322 na wannan doka.

Mai shari Senchi ya yanke masu hukuncin watanni 12 a gidan kurkuku ko kuma su biya fansar N1,000,000.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel