'Union Bank' ya ce shine mamallakin N1bn da EFCC ta cafke a filin jirgin sama na Enugu

'Union Bank' ya ce shine mamallakin N1bn da EFCC ta cafke a filin jirgin sama na Enugu

- 'Union Bank' ya ce shine mamallakin N1bn da EFCC ta cafke a filin jirgin sama na Enugu

- A ranar Juma'a, EFCC ta sanar da cewa ta samu nasarar cafke wasu mutane guda biyu, a tashar filin jirgin sama na Akanu Ibiam da ke Enugu, dauke da tsabar kudi har $2.8m

- Sai dai Union Bank ya ce wannan ba laifi bane, da cewa hakan bai sabawa tsarin masana'antar bankuna ba, haka zalika 'yan kwangilar na da lasisi daga CBN

Daya daga cikin tsofaffin bankuna a kasar Afrika, 'Union Bank, a ranar Juma'a, ya bayyana cewa shine mamallakin wasu makudan kudade da hukumar EFCC ta ce ta cafke a filin tashi da sauka na kasa da kasa da ke Enugu.

Hukumar yaki da cin hanci da rasawa EFCC, a ranar Juma'a ta sanar da cewa ta samu nasarar cafke wasu mutane guda biyu, a tashar filin jirgin sama na Akanu Ibiam da ke Enugu, dauke da tsabar kudi har $2.8m (sama da biliyan daya, akan N360 kowacce dala).

Hukumar ta ce wadanda ake zargin sun bayyana cewa sun dauko kudaden ne daga dakin ajiya na 'Union Bank', a cikin babban kwagirin ajiye kudi, akan tsarin safarar kudi ta kwangila.

KARANTA WANNAN: Ministan tsaro ya amayar da ta cikinsa kan kashe kashen rayuka a Zamfara da Kaduna

'Union Bank' ya ce shine mamallakin N1bn da EFCC ta cafke a filin jirgin sama na Enugu
'Union Bank' ya ce shine mamallakin N1bn da EFCC ta cafke a filin jirgin sama na Enugu
Asali: Twitter

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawar, ta ce bincikenta na kna karkarewa akan cewar wannan safarar kudi ce ba bisa ka'ida ba.

Sai dai 'Union Bank' ya karyata wannan a matsayin laifi, yana mai cewa hakan bai sabawa tsarin masana'antar bankuna ba, haka zalika 'yan kwangilar na da lasisi daga babban bankin Nigeria (CBN).

A martanin da Union Bank ya yiwa hukumar EFCC a shafinsa na Twitter a daren ranar Juma'a, ya kalubalanci hukumar na sanar da wannan lamari ga jama'a cikin gaggauwa, ba tare da bari sai ta kammala gudanar da bincike ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel