Ya zama wajibi a kori Ramos, Modric, Mercelo idan ana so na dawo Madrid - Mourinho
- Jose Mourinho ya bayyana sharuddansa, wadanda yake so a cika masa ma damar ana so ya koma Real Madrid
- Mourinho ya bukaci a kori 'yan wasan ne saboda a cewarsa, sune ke hana masa rawar gaban hantsi
- Rahotanni na hasashen cewa Karim Benzema, Marcelo, Sergio Ramos, Isco da Luka Modrid, sune wadanda Mourinho ke son a kora
Rahotanni daga kafar watsa labarai ta 'Express', na cewa korarren shugaban kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Jose Mourinho ya bayyana sharuddansa, wadanda yake so a cika masa ma damar ana so ya koma Real Madrid.
A ranar Talata, mataimakin shugaban kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ed Woodward ya shaidawa tsohon shugaban Chelsea cewa lokacin sa ya zo karshe a Old Trafford.
Mourinho ya bar Manchester United bayan sha kashi a hannun Liverpool da ci 3-1, wanda ya sa United ta samu maki 19, tare da komawa kasan aboka hamayyarsu a gasar Firimiya.
KARANTA WANNAN: Na shirya yadda zan samu biliyoyi daga garkuwa da mutane - Wanda ake zargi
Sai dai a yunkurin da ake yi na ganin Mourinho ya koma Real Madrid, tsohon shugaban kungiyar kwallon kafar na Intermillan, ya bukaci a kori wasu 'yan wasa daga kungiyar, wadanda a cewarsa, sune ke hana masa rawar gaban hantsi.
Rahotanni na hasashen cewa Karim Benzema, Marcelo, Sergio Ramos, Isco da Luka Modrid, sune wadanda Mourinho ke son a kora, wadanda in banda Isco, sauran sun taka leda karkashin Mourinho a 2010-2013.
Sai dai wasu rahotanni na ganin cewa wannan bukata ta Mourinho da wuya ta samu karbuwa, wanda kuma zai iya hanshi komawa shugabancin Madrid, yayi da aikinsa na gaba, ka iya kasancewa a wasu kungiyoyin kwallon kafa na nahiyar turai ko wajen turan.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng