Mummunar gobara tayi barna a wata babbar kasuwa a Arewacin Najeriya

Mummunar gobara tayi barna a wata babbar kasuwa a Arewacin Najeriya

Da misalin karfe biyu saura na daren Juma'a ne wata gobara ta tashi har zuwa wayewar gari a babbar kasuwar keffi dake jihar Nasarawa.

Gobarar ta kone kayyaki na milyoyin nairori. Wata majiya ta ce har yanzu ba a san musabbabin gobarar ba.

Amma ya ce bala'in gobara a kasuwar ta Keffi ya zama wani abin al'ajibi domin duk shekara a daidai irin wannan lokaci sai wuta ta tashi a kasuwar.

Mummunar gobara tayi barna a wata babbar kasuwa a Arewacin Najeriya

Mummunar gobara tayi barna a wata babbar kasuwa a Arewacin Najeriya
Source: UGC

KU KARANTA: Jami'in gwamnatin Buhari yayi murabus

Shugaban karamar hukumar Keffi Alhaji Abdurrahman Sani Maigoro ya shaida mana cewar lokacin da suka sami labarin faruwar lamarin sun yi kokarin kiran jami'an kashe gobara na Keffi ba su samu zuwa ba, don haka bai yi kasa a gwiwa ba sai da ya kira ofishin kashe gobara na Abuja amma suka ba shi wasu dalilai na rashin tsaro, haka dai wutar ta cinye dukiya mai tarin yawa.

Sai dai ba a rasa samun bata gari da aka samu suna satar kayan mutane ba, yanzu haka dai suna hannun 'yan banga daga bisani aka mika su ga 'yan sanda.

A wani labarin kuma, Wasu masu sana'ar kayan nauyi mutum biyu watau Bashir Aliyu da Ali Usman sun shiga hannun jami'an 'yan sandan Najeriya bisa laifin yiwa hukumar kula da filayen jiragen Najeriya kutse da kuma kokarin satar karafan da suka kai Naira miliyan 180.

Majiyar mu ta bayyana mana cewa barayin sun samu shiga hukumar ta Federal Airport Authority of Nigeria ne ta wata barauniyar hanyar da ta lalace daga filin jirgin tunawa da Murtala Mohammed, jihar Legas.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel