Kwanaki kadan kafin zabe, Hukumar INEC ta nada sabuwar Sakatariya

Kwanaki kadan kafin zabe, Hukumar INEC ta nada sabuwar Sakatariya

Kimanin kasa da watanni biyu kenan kafin zaben gama-gari na shekarar 2019 da za'a gudanar a Najeriya, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar watau Independent National Electoral Commission, INEC, a takaice ta nada Rose Orianran-Anthony a matsayin babbar Sakatariyar hukumar.

Kamar yadda muka samu daga majiyar mu, Orianran an nada mukamin Sakatariyar ne na shekaru hudu masu zuwa kuma ta shafe akalla shekaru 28 tana aiki a hukumar kafin ta samu wannan matsayin.

Kwanaki kadan kafin zabe, Hukumar INEC ta nada sabuwar Sakatariya

Kwanaki kadan kafin zabe, Hukumar INEC ta nada sabuwar Sakatariya
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Yan APC 2,000 sun koma PDP a jihar Neja

Legit.ng Hausa ta samu cewa da yake kaddamar da ita akan sabon mukamin nata, SHugaban hukumar zaben ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya taya ta murna sannan kuma ya ja hankalin ta da cewar ta saka gaskiya a wajen gudanr da ayyukan ta ba tare da nuna bangaranci ba.

A wani labarin kuma, Wani daga cikin mukarraban gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kuma shugaban hukumar gudanarwar Ma'aikatar dake da alhakin samarwa tare da tabbatar da zaman lafiya da kuma sasanci a tsakanin 'yan kasar Najeriya watau Institute for Peace and Conflict Resolution a turance yayi murabus.

Shugaban hukumar gudanarwar watau Governing Council a turance, Sanata Muhammed Abba-Aji din dai ya gabatar da takardar murabus din sa ne ga sauran 'yan hukumar gudanarwar a ranar Alhamis.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel