Fusatattun matasa sun kashe wasu mutane 5 da ake zargi da kaiwa masu garkuwa tsegumi a Zamfara

Fusatattun matasa sun kashe wasu mutane 5 da ake zargi da kaiwa masu garkuwa tsegumi a Zamfara

- Fusatattun matasa sun kashe wasu mutane biyar da ake zargi da kaiwa masu garkuwa tsegumi a Zamfara

- Garin Danjibga ta fuskanci hare-hare da dama da sace-sace mutane

- Kwanan nan ne wata mata ta haifi dan jinjirinta, kasa da sa’o’i biyar bayan anyi garkuwa da ita

Wasu fusatattun matasa sun halaka wasu mutane biyar da ake zargi da kaiwa masu garkuwa da mutane tsegumi a kauyen Danjibga, karamar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara.

Garin Danjibga ya fuskanci hare-hare da dama da sace-sace mutane wanda ake zargin yan fashi da barayin shanu da kaiwa a yan kwanakin nan.

Fusatattun matasa sun kashe wasu mutane 5 da ake zargi da kaiwa masu garkuwa tsegumi a Zamfara
Fusatattun matasa sun kashe wasu mutane 5 da ake zargi da kaiwa masu garkuwa tsegumi a Zamfara
Asali: Depositphotos

Makonni uku da ya gabata, wata mata ta haifi dan jinjirinta, kasa da sa’o’i biyar bayan anyi garkuwa da ita. An sace ta ne daga gidan auranta yayinda take cikin ciwon nakuda.

A ranar Alhamis da ya gabata, shugaban karamar hukumar, Abdullahi Aliyu Abubakar yayi ikirarin cewa kimanin mutane 40 aka kashe sannan sama da mutane 1,700 ne suka zama marasa galihu a karamar hukumar cikin makonni biyu.

KU KARANTA KUMA: Atiku, Obi sun gana da kungiyoyin jama’a, sun amince da hada kai don damokradiyya

Mataimakin shugaban kasaramar hukumar, wanda ya kasance dan garin, Alhaji Aliyu Yunusa Danjibga ya fadama Daily Trust cewa an gano masu kai tsegumin ne bayan mutanen ganin sun fuskanci munanan hare-hare da dama, yace har yanzu akwai sauran mutane a hannun masu garkuwan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel