Yan kauyen Zamfara sun kashe mutane biyar dake taimakawa barayin mutane

Yan kauyen Zamfara sun kashe mutane biyar dake taimakawa barayin mutane

- Akalla mutane 5 ne da ake zarginsu da kai kwarmato ga masu garkuwa da mutane suka gamu da ajalisnu a kauyen Danjibgam karamar hukumar Tsafe

- Al'ummar Danjibga sun dade suna fama da hare hare daga 'yan ta'adda, da kuma musifar masu garkuwa da mutane da suka hanasu sakat

- Shugaban karamar hukumar, Alhaji Aliyu Abubakar, ya bayyana cewa akalla mutane 40 ne aka kashe, yayin da mutane 1,700 suka rasa muhallansu

Akalla mutane 5 ne da ake zarginsu da kai kwarmato ga masu garkuwa da mutane suka gamu da ajalisnu a kauyen Danjibgam karamar hukumar Tsafe, inda a'ummar kauyen suka dauki hukunci a hannunsu, na aika mutanen barzahu.

Al'ummar Danjibga sun dade suna fama da hare hare daga 'yan ta'adda, da kuma musifar masu garkuwa da mutane da suka hanasu sakat, tare da kuma hare haren da barayin shanu suke kaiwa yankin nasu.

A makwanni uku da suka gabata, wata mata, ta haifi santalelen jaririnta a tantin masu garkuwa da mutanen, wacce suka sace a cikin gidan mijinta na aure, ba tare da sun duba halin da take ciki na nakuda ba.

KARANTA WANNAN: Sabon hari: Yan bindiga sun kashe mutane 25 a Zamfara

Yan kauyen Zamfara sun kashe mutane biyar dake taimakawa barayin mutane

Yan kauyen Zamfara sun kashe mutane biyar dake taimakawa barayin mutane
Source: Facebook

A ranar Alhamis din data gabata, shugaban karamar hukumar, Alhaji Aliyu Abubakar, ya bayyana cewa akalla mutane 40 ne aka kashe, yayin da mutane 1,700 suka rasa muhallansu a karamar hukumar, a cikin makwanni biyu kacal.

Mataimakin shugaban karamar hukumar, wanda shima mazaunin yankin ne, Alhaji Aliyu Yunusa Danjibga, ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa an cafko wadanda ke kaiwa masu garkuwa da mutanen bayanai kan wanda zasu kama, bayan da hakurin al'ummar ya kare kan yadda ta'addanci ke ci gaba da karuwa a yankin.

"Har zuwa yanzu, akwai mutane da dama da suke tsare a hannun masu garkuwa da mutanen, wasu kuma sun samu 'yancinsu bayan da aka biya kudin fansarsu," a cewarsa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel