Sabon hari: Yan bindiga sun kashe mutane 25 a Zamfara

Sabon hari: Yan bindiga sun kashe mutane 25 a Zamfara

- Wasu da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne, sun kashe mutane 25 a wani hari da suka kai wasu kauyuka biyu da ke cikin karamar hukumar Birnin Magaji, a jihar Zamfara

- Mazauna yankin da lamarin ya shafa, sun bayyana cewa a yammacin ranar Alhamis, 'yan bindigar suka kai harin haye a akan babura

- Sai dai kakain rundunar 'yan sanda na jihar Zamfara, Muhammad Shehu, ya ce mutane 5 ne aka kashe, kuma tuni rundunar ta tura jami'anta, inda aka kwantar da tarzomar

Rahotannin da Legit.ng ta samu daga Daily Trsut na nuni da cewa, a ranar Alhamis, wasu da ake kyautata zaton cewa 'yan bindiga ne, sun kashe mutane 25 a wani hari da suka kai wasu kauyuka guda biyu da ke cikin karamar hukumar Birnin Magaji, a jihar Zamfara.

Mazauna yankin da lamarin ya shafa, sun bayyana cewa a yammacin ranar Alhamis, wasu 'yan bindiga haye a akan babura sun bude wuta ga manoman dankalin hausa, da ke aiki a gonakinsu a kauyen Garin Halilu, inda suka kashe mutane 9 nan take.

Rahotanni sun bayyana cewa da misalin karfe 5 na yamma, 'yan bindigar suka sake komawa kauyen inda suka sake kashe wasu mutane 3, a lokacin da ake kokarin binne gawarwakin mutane 9 da suka kashe da farko.

KARANTA WANNAN: Hutun Shekara: Majalisar dattijai ta dake zama har sai 16 ga watan Janairu, 2019

Sabon hari: Yan bindiga sun kashe mutane 25 a Zamfara

Sabon hari: Yan bindiga sun kashe mutane 25 a Zamfara
Source: UGC

Sai dai kakain rundunar 'yan sanda na jihar Zamfara, Muhammad Shehu, ya ce mutane 5 ne aka kashe, kuma tuni rundunar ta tura jami'anta, inda aka kwantar da tarzomar.

A hannu daya kuwa, shugaban kasaramar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara, Aliyu Abubakar, ya shaidawa Daily Trust cewa akalla mutane 40 ne aka kashe, yayin da mutane 1,700 suka rasa gidajensu a karamar hukumarsa, cikin makwanni biyu kacal.

Ya ce akalla garuruwa biyar ne aka kakkabe a hare haren da 'yan ta'adda da barayin shanu suka kai karamar hukumar a cikin makwanni biyun, wanda kuma ya tilasta da yawan mazauna yankuna yin gudin hijira zuwa shelkwatar karamar hukumar don samun mafaka.

Garuruwan da lamarin ya shafa sun hada da Asaua, Kwadawa, Dogon Kawo, Mandaba, Yanza, Kulutu, Sakkya da kuma Fagin Dakai, duk a shiyyar kudanci Tsafe.

Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel