Rikicin cikin gida: Buhari ya bukaci kawo karshen rikice-rikicen APC a fadin Nigeria

Rikicin cikin gida: Buhari ya bukaci kawo karshen rikice-rikicen APC a fadin Nigeria

- Shugaban kasa Buhari ya roki masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC da su yi aiki tukuru don kawo karshen rikicin da jam'iyyar ke fama da shi

- Shugaban kasar ya gabatar da wannan bukata ne don baiwa jam'iyyar APC damar dinke barakarta tare da samun ansara a zabukan 2019

- Haka zalika, shugaba Buhari ya ce akwai babban gida da zai iya daukar duk wani mamba na jam'iyyar ACP kuma kofa a bude take ga masu sha'awar shiga

Biyo bayan rikice rikicen cikin gida na jam'iyyar APC da yaki ci yaki cinyewa a fadin kasar, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da su yi aiki tukuru don kawo karshen rikicin da jam'iuyar ke fama da shi don samun nasarar zaben 2019.

A cewar wata sanarwa daga hannun Garba Shehu, babban mai tallafawa shugaban kasar a fuskar watsa labarai da hulda da jama'a, da ya rabawa manema abarai a ranar Alhamis, shugaban kasar ya kawo wannan bukatar ne a daren ranar Laraba, yayin da ya karbi bakunfin wata kungiya ta APC, da suka hada da Farfesa Hafiz Abubakar, tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano wanda ya koma APC bayan shigarsa jam'iyyu da dama.

A jawabinsa na yiwa jagororin jam'iyyar maraba da dawowa APC, shugaban kasa Buhari ya ce akwai baban gida wanda zai iya daukar kowa, kana ya yi masu alkawarin tattaunawa da shuwagabannin jam'iyyar na kasa da na jihar Kano, akan cusa wadanda suka koma jam'iyyar cikin harkokokin yakin zaben 2019.

KARANTA WANNAN: Kasafin kudin 2019 da Buhari ya gabatar kamar takarda ce da babu rubutu a ciki - Saraki

Rikicin cikin gida: Buhari ya bukaci kawo karshen rikice-rikicen APC a fadin Nigeria

Rikicin cikin gida: Buhari ya bukaci kawo karshen rikice-rikicen APC a fadin Nigeria
Source: UGC

A cewar sanarwar, a kari kan Farfesa Hafiz, dan a mutum sanata Rabiu Kwankwaso, wanda ya yi murabus daga mataimakin gwamna Abdullahi Ganduje, akwai sauran jigogin jtafiyar da suka dawo APC, da suka hada da tsohon babban manajan hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa, Arch. Aminu Dabo.

Sauran sun hada da tsohon babban Ma'aji na kasa, Bala Mohammed Gwagwarwa; mashawarci ga Kwankwaso kan harkokin tsaro, Janar Danjuma Dambazau (rtd); Injiniya Muazu Magaji, wandada gaba dayansu sun kasance daga cikin jigogin tafiyar Kwankwaso, kai harma da Sanata Isa Zarewa, wanda ya bar jam'iyyar sakamakon rashin jin dadin zabukan fitar da gwamani da APC ta gudanar.

Tawagar ta samu ganawa da shugaban kasa Buhari karkashin jagorancin gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel