Kuma dai: Mahara sun kashe mutane da dama a wasu kauyukan jihar Zamfara

Kuma dai: Mahara sun kashe mutane da dama a wasu kauyukan jihar Zamfara

- Wasu yan bindiga sun kai mumunan hari a wasu kauyukan jihar Zamfara

- Maharan sun kaddamar da harin ne a garin Haladu, garin Kaka da Nasarawa Godal da ke karamar hukumar Birnin Magaji

Wasu yan bindiga sun kashe mutane da dama a kauyukan garin Haladu, garin Kaka da Nasarawa Godal da ke karamar hukumar Birnin Magaji a jihar Zamfara, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Birnin Magaji can ne mahaifar Ministan Tsaro, Mansur Dan-Ali, kuma mahaifin sa ne Hakimin Masarautar Karamar Hukumar.

Kuma dai: Mahara sun kashe mutane da dama a wasu kauyukan jihar Zamfara

Kuma dai: Mahara sun kashe mutane da dama a wasu kauyukan jihar Zamfara
Source: Depositphotos

Wani mazaunin daya daga cikin kauyukan da baya so a fadi sunan sa ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 20 ga watan Disamba.

Mazaunin yace yan bindigan sun far wa kauyen Garin Haladu inda suka kashe manoma 12 a gonakin su da karfe daya na ranar Laraba.

KU KARANTA KUMA: Tsohon gwamnan jihar Niger Aliyu ya zargi APC da shirin magudi a zaben 2019

Ya kara da cewa a dalilin wannan hari da dama sun sami rauni a jikinsu sannan suna samun kulan da suke bukata a asibiti.

Bayanai sun nuna cewa wannan ba shine karo na farko ba da mahara ke kai wa kauyukan jihar Zamfara hari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel