Ganawar farfesa Hafiz Abubakar, dattawan Kwankwasiyya da Buhari cikin hotuna

Ganawar farfesa Hafiz Abubakar, dattawan Kwankwasiyya da Buhari cikin hotuna

A ranan Laraba, an kawo rahoton cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da wata tawagar tsaffin mambobin All Progressives Congress APC daga jihar Kano karkashin jagorancin gwamnan jihar Jigawa, Muhammadu Badaru.

Wadanda suka gana da Buharin sun ya kunshi tsohon mataimakin gwamnan jihar, Hafiz Abubakar; tsohon ma'ajin jam'iyyar APC, Bala Gwagwarwa da tsohon shugaban hukumar NPA, Aminu Dabo, Injinya Mu'azu Magaji, Janar Danjuma Dambazzau da Sanata Isa Zarewa.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya tabbatar da hakan da yammacin Alhamis, 20 ga watan Disamba inda yace:

"Shugaba Buhari ya hadu da tsaffin mambobin APC da suke hanyarsu ta komawa jam'iyyar a fadar shugaban kasa ranan 19 ga watan Disamba, 2018."

Ganawar farfesa Hafiz Abubakar, dattawan Kwankwasiyya da Buhari cikin hotuna
Ganawar farfesa Hafiz Abubakar, dattawan Kwankwasiyya da Buhari cikin hotuna
Asali: Facebook

Mun kawo muku rahoton cewa tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar, wanda yayi murabus a kwanakin baya ya koma jam'iyyar All Progressive Party (APC) bayan komawa jam'iyyar adawa ta PDP da kuma PRP.

Mai magana da yawun farfesa Hafiz Abubakar, AbdulWahab Sa'id ya ce maigidansa ya koma APC ne bayan wata ganawa da yayi da shugaba Muhammadu Buhari a daren Laraba tare da wasu abokan siyasan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

AbdulWahab wanda ya tabbatar da wannan labari a ranan Alhamis bai yi bayani kan abubuwan da suka tattauna akai amma yace akwai wasu shirye-shirye da sukeyi kan sauya shekar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel