'Dan Majalisa ya jefi Firai Minista da kwai yana tsaka da gabatar da jawabai a zauren Majalisa

'Dan Majalisa ya jefi Firai Minista da kwai yana tsaka da gabatar da jawabai a zauren Majalisa

A yayin da a nan gida Najeriya ihu ne kadai ya shiga tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da wasu 'yan majalisa masu adawa da gwamnatin sa, mun samu cewa lamarin ya sha bambam da yadda ta kasance a zauren majalisar kasar Albania.

Endri Hasa, wani majalisar tarayya ta gwamnatin kasar Albania, a yau Alhamis, ya jefe Firai Ministan kasar, Edi Rama, da kwayayen kaji yana tsaka da gabatar da jawabai a zauren majalisar.

Bayan tsawon kimanin watanni shida na rashin bayyana a gaban majalisar sakamakon dambarwar adawa da ta mamaye siyasar kasar, Firai Minista sai kwatsam saukar jifa ta kwan kaji ya ji a jikin sa da tsiyayar ruwan kwai ta dabaibaye taguwar sa da karni.

Cikin gaggawa fadawan sa suka yi masa kawanya akan mimbari na zauren majalisar ya na tsaka da gabatar dangane da zangar-zangar da wasu dalibai suka gudanar cikin kasar a kwana-kwanan nan.

'Dan Majalisa ya jefi Firai Minista da kwai yana tsaka da gabatar da jawabai a zauren Majalisa

'Dan Majalisa ya jefi Firai Minista da kwai yana tsaka da gabatar da jawabai a zauren Majalisa
Source: UGC

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, lamarin ya sanya aka jinkirta zaman majalisar har zuwa yammacin wannan rana ta Alhamis. Kakakin majalisar ya zartar da hukuncin dakatar da dan Majalisa Endri Hasa daga bayyana a gabanta har na tsawon kwanaki goma masu zuwa.

Tsananin adawar siyasa ta sanya dan majalisa Hasa ya yiwa Firai Ministan kasar tsaurin ido domin nuna goyon ga Daliban masu gudanar da zanga-zangar ta neman biyan bukatar su a hannun gwamnatin kasar.

KARANTA KUMA: Yiwa Shugaba Buhari Ihu a zauren Majalisa rashin tarbiya ce tsagwaranta - Gwamna Bello

Binciken manema labarai ya tabbatar da cewa, Dalibai na ci gaba da gudanar da zanga-zanga a fadin kasar da ke yankin Kudu maso Gabashin Turai domin nuna rashin amincewar su kan tsadar kudin Makaranta da gwamnati ta tsawwala a kansu, inda suke fafutikar neman rangwami.

Domin nuna tsagwaran adawarsa cikin zolaya, tsohon shugaban kasar Sali Berisha, ya yi wani rubutu a shafin sa na zauren sada zumunta inda ya bayyana cewa, jefe Firai Minista da kwayayen kaji sakon gaisuwa ne da kuma taya murna yayin gabatowar bikin Kirsimeti da kuma sabuwar shekara.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel