Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dira jihar Kano

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dira jihar Kano

- Shugaba Buhari ya isa jihar Kano daga Abuja

- Gwamnan jihar, mataimakin gwamnan da manyan jami'an gwamnati sun tarbesa

- Zai kaddamar da wasu ayyuka a jihar

Labarin da ke shigowa da duminsa na nuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhar ya isa jihar Kano da yammaci rana Alhamis, 20 ga watan Disamba 2018 domin halartan bikin yaye daliban makarantan yan sanda da kuma kaddamar da wasu gagaruman ayyuka da gwamnatin jihar Kano ta kammala.

Shugaba Buhari ya samu kyakkyawan tarba daga gwamnatin jiharinda aka shirya masa faretin jami'an tsaro a filin jirgin saman Aminu Kano dake jihar.

Mun kawo muku rahoton cewa shugaba Muhammadu Buhari zai je makarantar horas da 'yan sanda dake a garin Wudil ta jihar Kano a ranar Alhamis din nan mai zuwa domin halartar bikin yaye sabbin daliban da makarantar ta horas tare da bayar da lambobin yabo ga zakakurai a cikin su.

Sai dai kuma ana tunanin bai ji dadin zargin da ake yiwa Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ba domin kuwa ana sa ran ba zai je gidan gwamnatin jihar ba a ranar duk kuwa da kasancewar su a jam'iyya daya kuma al'ada ta gaji haka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel