Ko kallon kasafin kudin ba zasuyi ba - Yan majalisan dattawa sun tafi hutu sai sabuwar shekara

Ko kallon kasafin kudin ba zasuyi ba - Yan majalisan dattawa sun tafi hutu sai sabuwar shekara

- Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Honourable Justice Uwani Musa Abba Aji, JCA a matsayin mai shari’a a kotun kolin Najeriya

- Yan majalisan sun tafi hutun Chrismeti da Sabuwar shekara har na tsawon wata daya

- Da yiwuwan ba zasu duba kasafin kudinba sai bayan zabe

Majalisar dattawan Najeriya ta alanta kulle majalisar na wannan shekara zuwa ranan Laraba, 16 ga watan Junairu, 2019.

Wani ya biyo bayan gabatar da kasafin kudin 2019 da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar a rana Laraba, 19 ga watan Disamba, 2019.

Shugaban masu rinjaye a majalisar, Sanata Ahmad Lawan, ya mika bukatar kulle majalisar kuma Sanata Philip Aduda ya jaddada.

KU KARANTA: Gudaji Kazaure ya kwancewa 'yan PDP zani a kasuwa kan Buhari

Gabanin kulle majalisar, Majalisar dattawan Najeriya a ranar Alhamis, 20 ga watan Disamba ta tabbatar da nadin Honourable Justice Uwani Musa Abba Aji, JCA a matsayin mai shari’a a kotun kolin Najeriya bayan tattaunawa da dama.

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, wanda yayi magana bayan tabbatar da nadin ya taya Abba-Aji murnar wannan sabon mukami da ta samu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel